Cancanta za mu zaba a shekarar 2023 – Daliban Arewa

Haruna Yusuf Abba,

Kungiyar Daliban Tunawa da Sardaunan Sakkwato Sa Ahmadu Bello ta manyan makarantun Arewa, ta yi matsaya cewa za ta dubi cancanta ce, kan wanda zai shugabanci kasar nan a zaben shekarar 2023. Kungiyar ta dauki wannan matsaya ce a wajen wani taro da ta gudanar a garin Jos.

Da yake yi wa wakilinmu karin bayani kan matsayar da kungiyar ta dauka, Shugaban Kungiyar,  Haruna Yusuf Abba  ya ce sun dauki matsayar a zabi  mutumin da ya cancanta wanda zai magance matsalolin da suke damun Arewa na Boko Haram da garkuwa da mutane da rashin makarantu da asibitoci, domin ita ce mafita.

“A zaben shekara ta 2023  za mu nemi shugaba ne wanda ya cancanta, don ganin ya magance mana matsalolin da suke damunmu, ba tare da lura da addininsa ko kabilarsa  ko daga wajen da ya fito ba,” inji shi.

Shugaban kungiyar ya ce babban dalilin da ya sanya  suka dauki wannan matsaya, shi ne ganin yadda yanayin kasar nan ya juya  na zaben mutum ba don cancanta ba, sai don  addini ko kabila ko yanki. Ya ce siyasa ana duba wanda ya cancanta ne, domin tana taba rayuwar dan Adam ne baki daya.

Ya ce “Matukar ba mu zabi mutanen da suka cancanta ba a zaben shekara ta 2023 ta hanyar duba irin abubuwan da suka yi a baya, za mu ci gaba da kasancewa cikin matsala a kasar nan.”

ADVERTISEMENT

Shugaban ya ce matasa ne wakilan al’umma a  Najeriya, don haka ya kamata su fito su shiga siyasa, su bada gudunmawarsu  amma ba su zamo ’yan bangar siyasa ba.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya