✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Canjin sheka a tsakanin ’yan siyasar kasar nan alheri ne ga dimokuradiyya? 1

Canjin sheka a tsakanin ’yan siyasar kasar nan alheri ne ga dimokuradiyya? 5… Yadda canjin sheka ya zama ruwan dare a tsakanin ‘yan siyasar kasar…

Canjin sheka a tsakanin ’yan siyasar kasar nan alheri ne ga dimokuradiyya? 5…

Yadda canjin sheka ya zama ruwan dare a tsakanin ‘yan siyasar kasar nan ta sa wakilanmu suka bazama don jin ra’ayoyin jama’a a kan haka. Ga ra’ayoyin kowane daga  ciki kamar haka

Canja shekar ’yan siaysa ba alheri ba ne – Inusa Ibrahim

Sunana Inusa Ibrahim. Da farko ka ga ‘yan siyasar kasar nan sun dade suna yaudararmu. Shi ya sa muke tunanin cewa tunda suka fara canja shekar nan, gaskiya ba lallai ba ne su nuna gaskiya. Za su ci gaba da yi mana abin da suka saba yi ne can baya. Idan ka tsaya ka yi la’akari za ka gano cewa kowannensu fa yana canja shekar don kansa ne ba don amfanin talaka ba. Yana yi ne don kansa da iyalensa. Da a ce don talaka suke canja shekan, kaga za mu iya ce alheri ne ga bangaren siyarar kasar nan da al’ummar ta baki daya. Amma sai ya kasance don kansu suke yi. Saboda haka a gani na dai canja shekan ba alheri ne ga kasannan ba.