✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Casillas zai yi takarar Shugaban Hukumar FA ta Spain

Tsohon golan Spain da kulob din Real Madrid Iker Casillas ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar  Shugaban Hukumar Kwallon Kafa (FA) ta Spain da zai…

Tsohon golan Spain da kulob din Real Madrid Iker Casillas ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar  Shugaban Hukumar Kwallon Kafa (FA) ta Spain da zai gudana nan ba da dadewa ba.

Casillas wanda ya samu nasarar lashe manyan kofuna a Spain da kulob din Real Madrid ya kamu da matsalar ciwon zuciya ne a watan Mayun bara lokacin da yake yin kwallo a kulob din FC Porto na Fotugal.

Tun daga wancan lokaci bai warke ba al’amarin da ya sa ya daina kwallo kuma yake yunkurin yin takarar shugabancin hukumar a bana.

Daga cikin nasarorin da Casillas ya samu lokacin da yake yi wa Spain kwallo akwai lashe kofunan Nahiyar Turai wato Euro a shekarar 2008 da 2012 da kuma lashe Kofin Kwallon Kafa na Duniya a 2010 da aka yi a Afirka ta Kudu.  Sannan ya lashe kofuna da dama a kulob din Real Madrid da suka hada da La-Liga da Copa del Rey da Zakarun Turai da sauransu.