Categories
Fitattun mata

‘Zan magance matsalar ruwan sha a yankunan karkarar Fika’

Sabuwar zababbiyar Shugabar Karamar Hukumar Fika a jihar Yobe, Hajiya Halima Joda Kyari Alkamar Gudi, ta sha alwashin magance matsalar karancin ruwan sha a yankunan karkara dake yankin.

Ta bayyana hakan ne a yayin wani rangadin gani da ido da ta kai garuruwan Janga da Boza da suke fama da matsalar tsaftataccen ruwan sha.

Ta ce garuruwan sun jima suna fama da matsalar inda kafin ta bar garuruwan ta dauki alkawarin cewa za ta yi dukkan mai yuwuwa don shawo kan matsalar.

Wasu jama’ar garin sun bayyana jin dadin su kan ziyara ta Shugabar sannan suka yi mata addu’ar fatan alkhairi da kuma yaba mata a matsayin mace shugaba abar koyi.

Categories
Fitattun mata Manyan Labarai

Matan da suka fi tashe a Najeriya a 2020

Yayin da ake ban kwana da shekarar 2020, Aminiya ta yi waiwaye kan wasu mata da labaransu suka yi tambari tare da daukar hankali a Najeirya a cikin shekarar.

Labaran wadananan mata guda 10 sun yi tashe a shekarar ce saboda jarumta, fice, ce-ce-ku-ce da sauransu daga fannonin rayuwa daban-daban na rayuwa. Ku biyo mu:

1. Tolulope Arotile

Marigayiyi Tolulope Arotile

Labarin mace ta farko mai tuka jirgin saman yaki a Najeriya, Flight Officer Tolulope Arotile ya yi tashe a 2020 bayan da ta kai hare-hare da jirgi a kan maboyan ’yan bindiga a yankin Arewa ta Tsakiya.

Hafsar Sojin Sama, mai shekaru 20 na cikin aikin yaki da ’yan bindigar ne labarin rasuywarta ya karade Najeriya.

Kasar ta kadu da rasuwar Tolulope wadda ta samu yabo a matsayin jaruma mai kishin kasa kuma abin koyi ga matasa musamman mata.

Tolulope ta gamu da ajalinta ne a Barikin Sojin Sama da ke Kaduna, sakamakon hatsarin mota.

2. Rahama Sadau

Jarumar masan’antar Kannywood Rahama Sadau ta karade shafukan sada zamunta bayan da wani ya yi tsokacin batanci ga Manzon Allah (SAW) a kan hoton da ta wallafa a shafinta na Twitter.

Batancin ya jawo caccaka da la’anata har sai da jarumar ta fito a wani bidiyo ta bayar da hakuri tare da wanke kanta da cewa ba za ta taba yarda ta yi abin da zai kai ga batanci ga Manzon Allah (SAW) ba.

Rahama Sadau a lokacin da take ba da hakuri ga al’ummar Musulmi.

Bayan wani bawan Allah ya aike wa ’yan sanda takardar korafi kan lamarin batancin, an yi ta baza jita-jitar cewa ’yan sanda sun tsare ta kuma kotu ta daure ta.

Rahama Sadau ita ce mace daga yankin Arewacin Najeriya da aka fi neman bayanai a kanta a Google a 2020, abin wasu ke gani yana da nasaba da ce-ce-ku-cen da ya shafe ta.

3. Aisha Yesufu

Daya daga cikin jagororin BringBackOurGirls masu neman dawo da ’yan matan Chibok ta kara yin tashe a 2020 musamman lokacin zanga-znagar #EndSARS.

Labarinta ya karade shafukan zumunta musmman bayan ganin ta sanye da zumbulelen hijabi a cikin masu zanga-zangar ta neman rushe sashen ’yan sandan SARS da ake zargi da cin zalin jama’a musamman matasa.

Yayin da wasu suka yabe ta  da cewa ta yi abin kai, wasu kuma sun yi ta caccakar ta da cewa ana amfani da ita ne domin rusa Arewa.

Lamarin ya kai sai da ta sanya a shafinta na Twitter cewa ana yi mata muguwar addu’a a masallatai saboda zanga-zangar.

Aisha Yesufu a lokacin

Aisha Yesufu ta kuma yi kaurin suna wurin sauke wa gwamnati lodi ta hanyar caccaka.

A karshe-karshen 2020, ta yi ta musayar yawu a Twitter da Mashawarcin Shugaba Kasa kan Shafukan Zumunta, Bashir Ahmed, game da gazawar Gwamnati.

4. Aisha Buhari

Matar Shugaban Kasar Najeriya, Aisha Buhari na gaba-gaba cikin wadadan suka karade shafukan zumunta a shekarar.

Jami’an tsaronta sun bude wuta a cikin Fadar Shugaban Kasa bayan cacar baki tsakaninta da hadimi kuma dan uwan Shugaba Buhari, Sabi’u wanda aka fi sani da Tunde.

Jijiyoyin wuya sun tsahi ne a lokacin da ta yi takakkiya zuwa gidanshi a Fadar Shugaban Kasa don ta sa shi ya killace kansa bayan dowarsa da Legas, inda a lokacin cutar coronavirus take ganiyarta.

Shi kuma ya ce sam, Shugaban Kasa ya sahale masa, lamarin ya da kai ga cacar baki a tsakaninsu.

Da cacar bakin ta yi zafi ne masu tsaronta suka fara harbi (abin da ba a taba ji ba a Fadar) shi kuma ya ketara katanga ya arce.

Shugaban ’Yan Sandan Najeriya ya janye masu tsaron nata, matakin da ita kuma ta yi ta kalubalantar sa a kai.

Hajiya Aisha Buhari

Aisha Buhari ta kuma yi tashe a shekarar bayan da ta wallafa wani sako da maudu’in #Acecijama’a da kuma #ArewaMuFarka.

Ana ganin sakon nata wanda ya yi tashe, hannunka mai sanda ne kan matsalar tsaro da ta addabi yankin Arewa ga gwamantin mijinta.

5. Maryam Booth

Bidiyon tsiraicin da aka fitar na jarumar Kannywood Maryam Booth ya ja ce-ce-ku-ce a kafafe daban-daban.

Maryam Booth ta zargi tsohon saurayinta, Deezel da fitar da bidiyon da ta ce an dauka ne shekaru da dama da suka wuce domin aibata ta.

Sai dai Deezel ya musanta zargin fitar da bidiyon mai tsawon dakika uku, kuma kara da cewa babu abin da yin hakan zai kare shi da shi.

Booth ta kuma yi tashe a shekarar bayan da ta lashe kyautar kyautar Jaruma Mace Mafi Iya Mara Baya a Kayutar Fina-finan Afirka (AMAA) na shekarar 2020.

Maryam Booth

Maryam Booth ta samu kyautar ce saboda rawar da ta taka a fim din ‘The Milkmaid’.

Ta doke wadda ta zo a matsayi na biyu, Chairmaine Majeri, wadda ta taka makamanciyar rawar a fim din ‘Mirage’sai kuma Linda Ejiofor a fim din ‘4th Republic’ a matsayi na uku.

 

5. Sadiya Umar-Farouk

Labarin kanzon kurege na auren Ministar Agaji Sadiya Umar Farouk da Babban Hafsan Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, Air Marshal Sadique Abubkar na daga cikin wadanda suka yi tashi.

Rade-radin aurenta da Sadique shi ne na biyu bayan makamancinsa da aka yi ta yadawa a bara cewa Shugaban Kasa Buhari ya angwance da ita.

Tuni dai Air Marshal Sadique ya karyata da ake yi ta bazawa cewa an yi auren ne cikin sirri a wani masallaci da ke unguwar Maitama a Abuja.

Ministar Agaji da Jinkai Hajiya Sadiya Umar Faruk
Ministar Agaji da Jinkai Hajiya Sadiya Umar Faruk

7. Fatima Ridabu

Labarin Fatima, diyar Nuhu Ribadu, tsohon Shugaban Hukumar  EFCC mai yaki da almundahada ya karade gari inda aka zarge ta da bayyana tsiraici a lokacin bikin aurenta.

Surutan da ta sha a shafukan zumunta bayan fitar hoton auren da ta sanya dogouwar riga fara mai shara-shara daga samanta ya kai ga sai da ta nemi afuwar jama’a.

“Kamarar rigar mai ruwan kasa da na sanya ce aka gani kamar fatata ce – ba zan taba yin haka ba,” inji Fatima Ribadu.

Fatima da minjinta (mairawani) tare da surukinta da wasu mahalarta daurin auren

Ta ci gaba da cewa, “Duk da haka na dauki laifin kunyatar da hakan ya jawo wa ’yan uwana da abokan arziki, na kuma dauki darasi.”

Sai dai amaryar ta Aliyu, dan tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakatar ta yi takaicin yaduwar hotunanta da ta ce a cikin gida suka dauka amma aka baza su a shafukan zumunta.

8. Maryam Sanda

Hukuncin kisa ta hanyar rataya da kotu ta yanke wa matar da ake zargi da kashe kashe mijinta, ya dauki hankali matuka.

Ra’ayoyi sun bambanta kan wadda aka yanke wa hukuncin wadda a lokacin take dauke da jaririyarta, diyar mijinta Bilyaminu da ake zargin ta kashe shi.

Maryam wadda ta fashe da kuka tare da sallallami bayan alkali ya karanta hukuncin ta dauka kara, amma Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da hukuncin.

Yanzu ana jiran shari’ar da ta daukaka zuwa Kotun Koli ne a kan hukuncin da kotunan suka yanke mata.

Maryam Sanda rike da diyarta, bayan fitowa daga kotu

9. Ngozi Okonjo-Iweala

Tsohuwar Ministarla Kudi da Tattalin Arziki, Ngozi Okonjo-Iweala ta zama babban labari a Najeriya da ma duniya bayan da ta shiga takarar Shugaban Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO).

Okonjo Iweala wadda ake gani saura kiris ta kai ga gaci ta samu goyon baya a cikin gida da kasashen duniya, inda Shugaba Buhari ya ce Najeriya na goyon bayanta kai da fata.

Wasu labarai sun yi ta cewa ta kai bantenta amma daga baya hukumar WTO ta ce da saura tukuna.

Tsohuwar Ministar Kudi da Tattalin Arzikin Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala

10. Hanan Buhari

Amfani da Jirgin Shugaban Kasa da Hanan, diyar Shugaba Buhari ta yi zuwa wani taro a Jihar Bauchi ya tayar da kura inda ’yan Najeriya suka yi ta tofa albarkcin bakinsu.

Daga baya dai Fadar Shugaban Kasa ta fito ta bayyana cewa ’ya’yan Shugaba Buhari na da damar yin amfani da jiragen Shugaban Kasa.

Bikin daurin auren Hanan ya yi tashe sosai a Najeriya inda wasu matasa biyu masoyanta kuma ‘yan a-mutunta suka bayyana.

Da kyar da jibin goshi aka samu aka shawo kan na farkon wanda ya yi yunkurin kashe kansa saboda ta yi aure, ya rasa ta.

Na biyun kuma ya ce ya rumgumi kaddara tunda bai samu cikar burinsa na auren ta ba, amma ya yi alkawarin shanu hamsin domin a yi shagalin bikinta.

Sai dai kowanne daga cikin matasan biyu babu wanda ya taba yin ido hudu da diyar Shugaban Kasar, wadda ta shafin zumunta kawai suka san ta.

Hasali ma ba budurwar kodaya daga cikinsu ba ce.

Categories
Addini Fitattun mata Kasashen Waje Manyan Labarai Ta'aziya

’Yar Shaikh Ibrahim Nyass ta rasu

Allah Ya yi wa Sayyada Maryam Shaikh Ibrahim Inyass rasuwa a Kasar Senegal.

Sayyada Maryam diya ce ga shahararen malamin Musulunci na duniya kuma jagoran Darikar Tijjaniya, Marigayi Shaikh Ibarhim Nyass dan kasar Senegal.

Ana yi wa Sayyada Maryam lakabi da Hadimar Alkur’ani wanda ta saudaukar da rayuwar kacokan wurin hidimar Alkur’ani Mai Girma.

Sayyada Maryam ita ce ta assasa cibiyar haddar Al’kur’ani ta Darul Kur’an a shekarar 1975.

A karkashin cibiyar, ta gina makaranta mai dalibai 1,600 a Dakar, babban birnin kasar Senegal.

Makarantar ta yaye dimbin mahaddata Alkur’ani daga kasar Senegal da makwabta irinsu Gambia da Guinea Bisau.

Marigayiyar ta kuma gina makarantar Majma’u Sheikh Ibrahim Nyass Alta’alimi a shekarar 1984 a Dakar.

Categories
Fitattun mata Manyan Labarai

Ana tsine min a masallatai saboda #EndSARS —Aisha Yesufu

Aisha Yesufu mai fafutikar kare hakkin dan Adam ta koka bisa tsinuwar da ta ce ana mata a masallatai bayan an idar da sallah.

Ta yi mamakin irin tofin Allah tsine da ake mata saboda fafukikar da take yi, duk da cewa ta yi hakan a lokacin mulkin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ba tare da an yi tir da ita ba.

“Na samu labarin cewa ana ta tsine min a masallatai!

“Mutane na ware lokacin idan sun idar da Sallah suna addu’ar tsinuwa a kaina.

“Ina tambayan su sau nawa suka tsine min a lokacin da nake irini wannan fafutika a lokacin Janathan?

Mai fafutikar ta wallafa hakan ne a shafinta na Twitter a ranar Juma’a 30 ga watan Oktoba, 2020.

Tun bayan da  Aisha Yesufu ta bukaci matasan Arewa su fito su shiga zanga-zangar #EndSARS mutane da dama ciki har da jaruman masana’antat fim ta Kannywood da wasu daidaikun mutane suka yi tir da kiran nata har wasunsu suka yi bidiyo suna mayar mata da martani.

Aisha Yesufu na daga cikin wadanda suka assasa fafutikar #BringBackOurGirls na neman ganin an dawo da ‘yan matan Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace.

Daga baya tafiyar ta yi ta fadada tare da shiga sauran na’ukan gwagwarmayan kwato ‘yancin dan Adam, musamman mata.

Categories
Fitattun mata Manyan Labarai

’Yar Najeriya na gab da zama shugabar WTO mace ta farko

Mace ta farko kuma ’yar Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala  na gab da zama Darakta-Janar na Cibiyar Kasuwanci ta Duniya (WTO).

Okonjo-Iweala, tsohuwar Ministar Kudi da Tattalin Arziki ta Najeriya ta samu goyn bayan 104 daga cikin mambobin WTO 164.

“A cikin ‘yan takaran, Dakta Ngozi Okonjo-Iweala daga Najeriya ce ke da gagarumar damar samun amincewar kowa. Nan gaba za a fara tattaunawa kan abin da za a yi na gaba”, inji Shugaban Babban Zauren WTO, David Walker, kamar yadda Kakakinsa Keith Walker ta ruwaito  shi bayan zamansu da suka yi a ranar Talata.

Da haka, za ta kafa tarihin zama mace ta farko a duniya kuma mutum na farko daga nahiyar Afirka da ya zama Shugaban WTO.

Ta samu rinjayen ne bayan ganawar sirrin da kungiyar ‘Troika’ karkashin jagorancin Walker jakadan kasar New Zealand, mai fada a ji a WTO ta yi da mambobin cibiyar.

Hakan ya ba ta damar samun rinjaye a kan abokiyar hamayyarta tilo, Ministar Zuba Jari ta kasar Koriya ta Kudu, Yoo Myung-hee.

Ranar Laraba, 28 ga Oktobo 2020 Troika ke sanar da zamanta Darakta-Janar ta WTO da amincewar mambobin cibiyar 164.

  • WTO: Okonjo-Iweala ta kafa tarahi

Ta dare kujerar ne a daidai lokacin da cibiyar ke cika shekara 25 kuma ita ce mace ta farko a fadin duniya da za ta jagoranci cibiyar.

Shugabancin da ta samu ya sa ta zama mace ta farko a duniya kuma mutum na farko daga nahiyar da ya zama Shugaban Cibiyar Kasuwanci ta Duniya.

Ta hau kujerar ne kafin cikar wa’adin ranar 7 ga watan Nuwamba na maye gurbin Roberto Azevedo dan kasar Brazil, wanda ya yi sauka daga mukaminsa a WOT a watan Agusta, shekara guda kafin cikar wa’adinsa.

  • Goyon bayan da ta samu

Manyan kasashen duniya sun ki bayyana wanda suke boyon baya a cikin ‘yan takarar a fili duk da cewa wasu kasashen Afirka da yankin Caribbean sun bayyana goyon bayansu ga Okonjo-Iweala.

A gida Najeriya ma, Shugaba Buhari da babban attajirin Afirka Alhaji Aliko Dangote sun bayyana goyon bayansu ga da tsohuwar ministar kudin.

A wani sako da ta wallafa a baya-bayan nan, ta ce, “Ina matukar godiya da samun goyon baya domin zama Daraktar-Janar na WTO daga manyan shugabanni a duniya irinsu Mary Robinson, Mo Ibrahim, Aliko Dangote, Strive Masiyiwa, (da sauransu).”

A ranar Talata Tarayyar Turai ta sanar da goyon bayanta ga ‘yar Najeriyar.

Kazalika kungiyar Tarayyar Afirka dungurungun da kasashe da dama daga yankin Pacific da Asiya sun goyin bayan ta jagoranci

Kwarewar Ngozi Okonjo-Iweala

Ngozi Okonjo-Iweala mai shekara 66, ita ce mace ta farko da ta zama Ministar Kudi a Najeriya kafin daga baya ta jagoranci ma’aikatar Harkokin Waje.

Tsohuwar ministar ta shafe shekara 25 tana aiki a Bankin Duniya a matsayin kwararriya a tattalin arziki da gudanar da kudade na kasa har ta zama Manajan-Darekta, a Bankin Duniya.

A halin yanzu tana daga cikin Majalisar Daraktocin Twittter kuma babbar jakadiya ce a Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) kan yaki da COVID-19.

Aikin da ke gabanta a WTO

Babban aikin da ke gabanta a WTO shi ne yin gyaran fuska ga manyan kararrakin da cibiyar ta daukaka.

Cibiyar ta samu tasgaro a yunkurin nata bayan Shugaban Amurka ya tadiye ta saboda rashin alkalai.

Wani babban aikin da ke gabanta kuma shi ne shiryawa da kuma gudanar da babban taron kasuwanci a 2021.

Categories
Fitattun mata

Rayuwar iyayena ta taimaka wa tawa —Yakolo Indimi

Yakolo Indimi ita ce ta assasa Gidauniyar Yakolo Indimi (YIF), Shugabar kamfaanin Fashion Café Global Enterprises kuma darekta a kamfanin mai na Oriental Energy Resources.

Ta yi ayyukan a bangarori da dama na gwamnati da kamfanoni, inda ta taka rawar gani wajen kyautata rayuwar jama’a ta hayar tallafawa da horas da mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa.

A zantawarta da Aminiya, Yakolo ta bayyana tarihin yadda ta fara taimakon jama’a, da kuma sha’awarta ga sana’o’i da ayyukan jinkai da sauransu.

Ban ga dalilin da Najeriya za ta rika shigo da man fetur daga waje ba – Indimi

Mun sasanta da tsohon mijina —Rahma Indimi

 

Iyalan Indimi na daga cikin manyan gidaje mafiya shahara a Najeriya. Yaya yanayin tasowarki a wannan babban gida?

Sunana Yakoko Indimi, diya ga Muhammad Indimi da Fatima kuma an Haife ni ne a Jihar Borno ranar 19 ga Maris, 1977.

Na yi karatun firamare a Makarantar Firamare ta Jami’ar Maiduguri, a Jihar Borno sannan aka kai ni makarantar kwana a kasar Masar inda na yi karantun sakandare boko da addini a El Nasr Girl College, da ke Alexandria, wadda na kammala a 1989.

Ina farin cikin samun hakan kuma ba zan taba mantawa ba saboda na koyi abubuwa da yawa.

Na yi karartu a Jami’ar Lynn, Boca Raton da ke Florida a kasar Amurka.

A nan na yi digirina na farko a fannin kimiyyar aikin likitanci sannan na yi digiri na biyu fannin gudunarwa na kasa da kasa.

A takaice tasowa a gida irin namu dama ce ga mutum na samun tarbiyya da tallafin da yake bukata.

 

Da jin irin makarantu da kika halarta, hakika kin samu kwarewa kan abubuwa da dama. Yaya kika fara yin aiki bayan dawowarki Najeriya?

 

Haka ne. Bayan na kammala yi wa kasa hidima a 2000, na samu aiki kamfnin mahaifina na Oriental Energy Resources, inda na yi aiki a sassa da kuma matakai daban-daban na tsawon shekara 20.

Yanzu ni darekta ce na rijiyar hakar mai ta OML 115.

 

Shin akwai wani wani kasuwanci na kashin kanki da kike yi?

Ai ko mutum yana aiki yana da kyau ya kasance yana da wata sansa’a, shi ya sa nake harkar ado da kwalliya wanda cikin ikon Allah a dan kankanin lokaci na samu nasibi da fice a harkar.

Shafin kawa ne na iyaye mata da masu manyan shekaru da ke son su caba  ado cikin walwala ba tare da wata takura ba.

 

Yawancin mutane girma zuwa musu ne tare da rauni. Yaya za ki kwatanta yin aiki a skekarunki yanzu?

Alhamdulillahi Allah Ya ba ni lafiya domin yanzu haka nakan yi aiki daga safe zuwa karfe biyar na yamma ba tare da alamar rauni ba.

Duk da shekaruna ba ni da wata damuwa; ina jin dadin jikina kamar wata ’yar karamar yarinya.

Me kike yi a lokacinki na nishadi?

Duk sadda ke da lokaci to na fi so in kasance tare da ’ya’yana. Da zarar sun dawo makaranta nakan kula da su, in bibiyi litattafansu in tabbatar cewa babu wata matsala.

Yara masu kuruciya sai an yi da gaske wajen dora su a kan hanya a tabbata suna kiyaye ibada, ina kuma sa ido a kan irin tarbiyar da na dora su a kai.

 

Me ya sa kifa fara aikin taimakon jama’a?

Tun ban kai haka ba na fara aikin taimaikon jama’a saboda koyi da yadda mahaifina ke taimakon mutane – shi babban abin koyi ne wurin tallafa wa jam’a.

Allah Ya yi masa dabi’a ta yawan kyauta. Yakan ce idan Allah Ya ba ka wani abu to ka rika bayarwa domin da zarar kana kyauta to Allah Zai kara maka fiye da abin da ka bayar. Shi ya sa na ke koyi da shi.

Idan ya ba ni kudin kashewa, nakan kyautar da rabi, ni kuma in yi amfani da rabi.

Na ci gaba da yin hakan saboda yakan sa min farin ciki fiye da abubuwa da dama a rayuwa don haka ba zan iya dainawa ba.

Tun ina ’yar karama nake yi kuma yadda samuna ke karuwa haka nake kara yawan abin da nake bayarwa.

Da hakan har na wayi gari tamkar mahaifina da mahaifiyata domin ita ma haka take, shi ya sa na dabi’antu da yin hakan saboda masu dabi’ar na zagaye da ni.

 

Shin kin taba samun lambar yabo daga wata kungiyar jinkai saboda taimako da kike yi?

Da farko dai ba ina yi ba ne domin wani ko wata kungiya ko hukuma ta yaba min.

Ina yi ne saboda Allah domin Shi ke bayar da mafificin sakayya.

Amma kasancewar mutane kan lura da duk abin da kake yi, an sha ba ni kyaututtuka da lambar yabo da suka burge ni.

Majalisar Dinkin Duniya ta ba ni lambar yabo a babban taronta na 74 a matsayin daya daga cikin masu yada zaman lafiya da kuma kare muradun cigaba wajen kawar da fatara.

Na yi mamaki, kana yin abu a sirrance amma duniya na gani tana yabawa. Hakan ya kara min kwarin gwiwar ci gaba da irin taimakon da nake yi.

 

Yaruka nawa kika iya magana da su?

Na iya yaruka da dama: Turanci, Larabci, Kanuri, da kuma Hausa, kuma kowannensu zan iya magana da shi babu wata gargada.

 

Mene ne sakonki ga sauran masu ayyukan taimakon jama’a?

Hakika suna da muhimmiyar rawar takawa wajen saukaka wa mabukata wahalhalun da suke ciki.

Ba wayon mutum ne ya sa Allah Ya yi shi mawadaci ba; wadanda ba su da shi kuma ba wai ba su da wayo ba ne.

Allah Mabuwayi Ya san hikimarSa ta yin ka mawadaci kuma dukiyarka ba alama ba ce ta cewa Allah Yana son ka fiye da wadanda ba su kai ka dukiya ba ko matalauta.

Mallakar dukiya ba ita ba ce taimakon mutane, dole sai mutum na da zuciyar yin taimakon.

Na sha ganin masu kudi da ba sa kaunar su yi taimako, na kuma ga talakawan da ke iya bayar da iya abin da suka mallaka domin su taimaka wa wasu.

Duk da haka yana da kyau masu hali su rika ganin taimakon mabukata a matsayin hakki ne a kansu.

Mutum na samun kwanciyar rai idan yana taimako.

Na kan ji farin ciki a duk lokacin da na bayar daga abin da na mallaka, watakila saboda na taso na ga iyayena na taimakon mutane ne shi ya sa.

Ina ba wa mawadata shawara su lura cewa wasu ba su samu wannan damar da Allah Ya ba su ba.

Akwai marayu da wadanda iftila’i da yaki da sauran abubuwa suka daidaita rayuwarsu.

Yana da kyau a taimaka musu domin su ma su samu kyakkyauwar fata da rayuwa mai nagarta.

 

Shin kina ganin sana’a ta fi dacewa idan aka kwatanta da aikin gwamnati ko na kamfani?

Kwarai kuwa! Akwai riba mai yawa a cikin sana’a musamman idan mutum ya samu kwarewar da ta dace.

An fi samun daukaka da sauri ta hanyar sana’a idan mutum ya tsare gaskiya sannan yana da hakurin da iya zama da mutane.

Wadannan abubuwa biyu suna da matukar muhimmanci ga duk mai yin sana’a.

Shawarata ga matasanmu da suka kammala digiri da masu yin kasuwanci shi ne su riki sana’o’i da fatar cewa za su yi nasara da yardar Allah, kuma in Allah Ya yarda za su dace.

Categories
Fitattun mata Tattaunawa

Hajara Sanda: Fadi-tashin zama farfesa mace a fannin jarida

Hajara Umar Sanda it ace mace ta farko da ta kai matsayin farfesa a sashen koyar da aikin jarida na Jami’ar Bayero da ke Kano.

A ’yan kwanakin nan wata kungiya mai suna MassMediaNG ta karrama ta a matsayin daya daga cikin mata farfesoshi goma a fannin koyar da aikin jarida a Najeriya.

A cikin wannan tattaunawar, ta yi bayanin irin gwagwarmayar da ta sha har ta kai ga matsayin, musamman kasancewarta Bahaushiya daya tilo mai sanya hijabi a jerin wadanda aka karrama din.

Ya ya ki ka ji da karramawar da aka yi miki a matsayin daya daga cikin mata farfesoshi a bangaren koyar da aikin jarida a Najeriya?

A ranar 26 ga watan Agusta na samu wani sako ta dandalin sada zumunta na WhatsApp a wayata, bayan na bude shi sai na ga wani bidiyo da ke dauke da mata farfesoshi guda goma da ke kan gaba a fannin koyar da aikin jarida a Najeriya.

Abin mamaki ne matuka, saboda ban ma san su waye suka shirya shi ba.

Na damu matuka da yadda aka ambaci sunana a ciki saboda ban kai ga zama cikakkiyar farfesa ba tukunna.

Sai na yi kokarin samun lambar wayar wanda ya kirkiri shafin na MassMediaNG wanda shi ma yana dab da zama farfesa a fannin, inda ya tabbatar min da cewa suna karrama matan da suka yi fice ba lallai farfesoshi ba; a’a har ma wadanda suke dab da zama.

Ya ce min sukan duba abin da ya bambanta su [matan] da sauran da zai sa su zama zakarun gwajin dafi tsakanin takawarorinsu tare da karrama su da kyauta yayin bikin da za su gudanar na bana mai taken ‘Ranar Samar da Daidaiton Mata ta 2020’.

Sun kuma hada da wasu farfesoshi guda biyu masu mukamin emeritus.

Ya kuma shaida min cewa baya ga wadannan, sun kuma zabe ni ne kasancewar ni ce mace ta farko da ta kai wannan matsayin a sashenmu na Jami’ar Bayero inda suka kalli hakan a matsayin wani abu da zai kara karfafa cigaban ilimin ’ya’ya mata a Arewacin Najeriya.

Sun kuma ce na bayar da muhimmiyar gudunmawa a bangaren aikin jarida.

Mu uku ne mata aka zaba daga Arewacin Najeriya: Daya daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, dayar daga Jami’ar Jos sai kuma ni.

Gaskiya na dauki hakan a matsayin wata muhimmiyar girmamawa.

Sun ce bangaren da na fi mayar da hankali a wajen bincikena (Batutuwan da Suka Shafi Lafiyar Mata a Arewacin Najeriya) ne ya fi burge su.

Kazalika, sun ce ina daya daga cikin mata kalilan a Arewacin Najeriya masu koyar da aikin jarida da suka sami tallafin karo karatu zuwa Fulbright a kasar Amurka.

Mene ne sirrin jajircewarki har kika kai ga wannan matsayin?

Akwai wani salon magana da ke cewa duk abin da namiji zai yi, mace ma za ta iya yi ko ma fiye da haka.

Na tsinci kaina a cikin irin wani wuri da maza suka yi wa kaka-gida yayin da ake da mata ’yan kalilan, hakan ya karfafa min gwiwa wajen kara zage damtse.

Na kuma kara samun kwarin gwiwa lokacin da na sami tallafin karo karatu na Fulbright a kasar Amurka domin yin digirin-digirgir dina.

Wani kuma abin da ya kara karfafa min gwiwa shi ne ina son zama abar koyi ga ’ya’ya mata a Arewacin Najeriya.

Shin akwai wani kalubale da kika ci karo da shi a wannan fadi-tashin?  

Farkon dauka ta aiki a matsayin malamar jami’a kalubale na farko da na fara fuskanta shi ne na yadda nake shiga.

Mutane da dama sun rika yi min kallon raini saboda yadda nake saka hijabi, inda wasunsu ma ke tunanin ba zan iya tabuka wani abin ku-zo-ku-gani ba.

Wannan babban kalubale ne a wuri na, wanda shi kansa ya sa dole in tashi tsaye wajen ganin na ba mara da kunya.

Bugu da kari, tafiyata zuwa Amurka ita ma ta zo min da kalubale kasancewar dole na tsallake na bar iyalaina.

Amma Alhamdulillahi sakamakon hadin kan da na samu daga mijina da mahaifiyata komai ya zo min da sauki. Ina matukar godiya gare su.

Wani kalubalen da kuma na sake fuskanta shi ne tafiyar hawainiya a karin matsayin da ya kamata a yi min a aiki bayan kammala karatun digirina na biyu a kan wani dalilin da bai taka kara ba ballantana ya karya.

Amma daga bisani kuma aka yi wa wani abokin aikina namiji da yake da makamanciyar matsala irin tawa a wani sashen. Ba zan taba mantawa da wannan ba.

Kazalika a shekara ta 2012 bayan dawowata daga Amurka bayan kammala digirina na uku, na dawo da kammalallen rubutuna wanda na yi a karkashin kulawar malamin da ya duba min aikin.

Amma bayan na dawo Najeriya sai aka yi watsi da ni da gangan na kusan shekaru biyu ba tare da an kira ni na zo na kare aikina ba.

Dalilin ke nan da ya sa na kammala a shekarar 2014 a maimakon 2012 ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.

A matsayina na mace, maimakon a karfafa min gwiwa duk da cewa na tafi na bar dukkan iyalaina na samu na kammala a kan lokaci, sai aka yi watsi da ni.

Shin akwai lokacin da kika taba jin kin kusa sarewa?

Babu. Mun shafe shakara biyar muna kokarin kammala karatun digiri na biyu, akwai daya daga cikin ’yan ajinmu ma da ya tafi kasar Ingila daga bisani kuma ya samu ya kammala karatunsa a watanni tara.

Amma ni ban taba sarewa ba. Ni na yi amanna da ci gaba da fafutuka har na kai ga cimma nasara.

Ta yaya kika kai ga cin nasara kan wadannan kalubalen?

Na yarda da jajircewa. Akwai dadi da rashin dadi a rayuwa, amma hakuri da jajircewa su ne mabudin nasara.

Mijina da mahaifiyata kuma sun taka muhimmiyar rawa wajen ba ni gudunmuwa.

Shin ya kika ji kan tafiya kasar waje kika bar iyalanki saboda neman ilimi? 

Kafin na kai ga samun tallafin karo karatun na Fulbright, mutane da yawa sun shaida min cewa ko na samu ba zan iya tafiya ba.

Lokacin da aka gayyace ni jarrabawar tantancewa wasu ma sai da suka nemi sare min gwiwa wai kada na je, kuma ko da na samu ma mijina ba zai bar ni na tafi ba.

Amma cikin ikon Allah mijina kasancewarsa lauya kuma mai fafutukar ilimin mata ya ba mara da kunya, ya tsaya tsayin daka wajen tallafa min har na kammala karatun.

Ko lokacin da ina can Amurkan sai da ya kawo min ziyara lokacin da na kusa kammalawa muka dawo tare.

Na kuma sami tallafi daga hukumar jami’a da kuma abokan aiki na da ke sama da ni a jami’ar.

Haka kuma ina yaba wa Sashen Al’adu na Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya saboda gagarumar damar da suka ba ni. Ina matukar godiya gare su gaba daya.

Me kike ganin ya kamata a yi don bunkasa ilimin ’ya’ya mata musamman a yankin da kika fito na Arewacin Najeriya?

Akwai wani salon magana da ke cewa in ka ilmantar da da namiji ka ilmantar da mutum daya ne, amma in ka ilmantar da ’ya mace, tamkar ka ilmantar da alumma ce baki daya.

Mun san cewa ilimin ’ya mace yana da muhimmanci musamman a Arewacin Najeriya inda lamarin tabarbarewar ya fi kamari.

Yawanci akan fake da talauci da jahilci wajen dora musu talla da yi musu auren wuri.

Dole gwamnati ta shiga lamarin ta hanyar bayar da ilimi kyauta a kowane mataki gare su a Arewa.

 Na shiga kungiyoyi masu zaman kansu da dama da ke fafutukar karfafa gwiwar mata, ciki har da kungiyar tsofaffin daliban makarantata ta Shekara (SHOGA) inda muka yi abubuwa da dama wajen inganta ta har ta kai ga mun gina mata dakin shan magani.

Bugu da kari, kungiyarmu ta tsofaffin daliban Jami’ar Bayero aji na 1992 ta yi ayyuka da dama na cigaban al’umma.

Ina kuma cikin wata gidauniya da take mayar da hankali wajen bayar da tallafin karo karatu ga dalibai musamman mata da kuma masu bukata ta musamman.

Shin kina kallon nasarar da kika samu a rayuwa a matsayin abin da zai taimaka wajen kawo karshen kallon da ake wa mata a Arewa?

E hakika, na tabbata, wannan kuma somin tabi ne ma.

Na yi amanna cewar sinadaran cin nasara su ne aiki tukuru, gaskiya, hakuri, tsayawa kan gaskiya da rikon amana da kuma uwa uba tsoron Allah.

Ina shawartar ’yan uwana mata da su kara kokari domin ganin su ma sun kawo karshen irin kallon da ake yi wa mata kuma a ji sunansu a duniya.

Categories
Fitattun mata

HOTUNA: Jana’izar mace mai tuka jirgin yaki ta farko a Najeriya

Kalli yadda aka yi jana’izar Tolulope Arotile, mace ta farko mai tuka jirgin sama na yaki a Najeriya wadda ta rasu sakamakon hatsarin mota a Kaduna.

An yi jana’izar hafsar sojin saman ce a Makabartar Sojoji da ke Abuja a ranar Alhamis 23 ga Yuli, 2020.

Sojoji sun rako gawar Tolulope Arotile kafin a sanya ta a makwancinta.
Hoto: Felix Onigbinde.
Ministar Harakokin Mata Pauline Tallen a wurin jana’izar. Hoto: Felix Onigbinde.
Yan uwanta tare da limaman addinin Kirista a lokacin jana’izar a Abuja.
‘Yan uwan marigayiyar cikin alhini a wurin jana’izarta a Makabartar Sojoji da ke Abuja.
Mata sojoji takwarorin Flying Officer Tolulope dauke da furanni domin bankwana gareta.
Bankwana ga marigayiyar ta haryar yin harbi sau 21 bisa al’adar sojoji.
‘Yar uwar Tolupe a wurin jana’izar kanwar tata.
Babban Hafsan Tsaron Najeriya Janar Abayomi Gabriel Olonisakin yana ajiye furen bankwana da karramawa a jana’izar Tolulope.
Shugaban Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar ya hannanta tutar Najeriya ga ‘yar uwar mai rasuwar bayan an binne ta.
Categories
Fitattu a labarun mako Fitattun mata Manyan Labarai

Tolulope: Ya kamata a binciki mutuwarta

‘Yar uwar mace ta farko mai tuka jirgin yaki a Najeriya Damilola Adegboye ta bukaci a yi bincike kan musababbin mutuwar kanwartata, Tolulope Arotile.

Damilola Adegboye, yayar marigayiya hafsan sojin sama Tolulope ta nuna shakku kan dalilin da aka bayar na rasuwar kanwarta, domin a cewarta, “ta yaya za a yi motar da ke juyowa da baya za ta iya kashe ‘yar uwarta”.

Ta ce “Mu ‘yan uwanta ba mu gamsu da dalilin da aka bayar na rasuwarta ba, rundunar soji kwararu ne wajen gudanar da bincike, saboda haka muna bukatar su yi binciken da zai gamsar da mu.

“A ranar mutuwarta ina tare da ita a dakin da take a kwance, wani ne ya kira ta a waya cewa ta dawo bakin aiki, ina kyautata zaton babban hafsan sojin sama ne, ba ta ji dadin kiran ba domin sai da ta yi kamar ba za ta amsa kiran ba, amma na ce mata zan kai ta a mota.

“Bayan sa’a guda da kiran ta da aka yi sai ga labari na gani ta yanar gizo cewa ta gamu da mummunan lamari ta mutu, taya zan yarda, yarinyar da ni na sauke ta a mota cikin sa’a guda”, inji ta.

Za a tuna da marigayiya Tolulope

A bangare guda kuma Majalsiar Dokokin Jihar Kogi inda Tolulope ta fito ta amince da kudurin dokar sanyan suna marigayiya Tolulope domin tunawa da ita saboda gagarumar gudunmuwarta wajen yakar ‘yan bindiga da sauran matsalolin tsaro a Najeriya.

Bayan amincewa da kudurin dokar wanda dan majalisa Kilani Olumo mai wakiltar mazabar Tolulope ta Ijumu ya gabatar, Majalisar ta bukaci gwamnatin jihar ta da gaggauta sanya sunan marigayiyar.

Abin da ya bambanta Tolulope

Tolulope ita ce hafsan sojin saman Najeriya ta farko mai tuka jirgin sama, kuma tana sahun farko a yaki da matsalar tsaro musamman a yankin Arewa ta tsakiya da Arewa maso Yammacin Najeriya.

Ita ce aka fara yayewa kai tsaye a matayin hafsan sojin sama, bayan Grace Garba wadda ta fara aikin tun daga matsayin kurtu har ta zama hafsa.

Babban burin Tolulope tun tana ‘yar karama shi ne tuka jirgin yaki kuma shi ne abin da ta mayar da hankali a kai a lokacin da take kwalejin soja.

Mahaifanta sun bayyana ta a matsayin mai tsananin kaifin basira da kuma kwazo.

Ta fara tuka jirgin yaki a shekarar 2017 bayan kammala karatu a kwalejin kananan hafsohin soja ta Najeriya (NDA) da ke kaduna, inda ta samu digiri a fannin Kimiyyar Lissafi.

Ta yi karatun firamare da sakandarenta a makarantar ‘ya’yan sojojin sama ta Najeriya da ke Kaduna.

Rasuwarta

Tolulope ta rasu sakamakon raunukan da ta samu a kanta a hatsarin mota da ya ritsa da ita a barikin sojojin sama da ke Kaduna.

Yayin sanar da rasuwarta, Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta bayyana kaduwa tare da kwatanta mutuwar a matsayin babban rashi

Rundunar ta yaba irin kwazon da Tolulope ta yi wajen yakar ‘yan fashin da sauran ‘yan bindiga a jihar Neja da yankin Arewa masu Yamma.

‘Yan Najeriya daga ko’ina sun yi ta juyayin rasuwarta tare da kwatanta ta a matsayin jaruma.

Categories
Fitattun mata Kananan Labarai Ta'aziya

Yadda ’yan Najeriya ke juyayin rasuwar Arotile

’Yan Najeriya na ta nuna alhininsu game da mutuwar ’yar kasar ta farko mai tuka jirgin yaki Tolulope Arotile wadda ta rasu tana ‘yar sheakra 23 sakamakon hatsarin mota a jihar Kaduna ranar 14 ga Yuli, 2020.

’Yan kasar na ta mika sakonnin ta’aziyyar rasuwar hafsar sojin saman ne a Twitter da sauran shafukan sada zumunta, kamar haka:

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyyarsa ga mutuwar Tolulope Artile matukiyar helikwaftan yaki ta farko a Najeriya.

Kamar yadda mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na twitter@GarShehu cewa shugaban ya yi addu’a ga iyalanta na fatan jurewa wannan babban rashi da su ka yi.

Shugaba Buhari ya jinjina wa Arotile kan kwazonta a filin yaki domin kare kasarta daga ‘yan tada kayar baya.

Sanata Shehu Sani @ShehuSani, tsohon Dan Majalisar Dattawan mai wakilarta Kaduna ta Tasakiya Sanata Shehu Sani ya ce, “Abin takaici lokaci kadan bayan na wuce ta barikin sojin sama da ke Kaduna, hatsarin ya faru wanda ya yi ajalin matukiyar jirgin yaki ta farko ’yar Najeriya Tolulope Arotile. Babban rashi ga Najeriya. Allah Ya jikan ta”.

Shi ma tsohn Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa,

Ike Ekweremadu @iamekweremadu:

Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu ya ce: “Ta’aziyyata ga @NigAirForce da iyalan Tolupe, mace ta farko ‘yar Najeriya matukiyar jirgin sama wadda ta mutu a hatsarin mota a barikin sojin sama na Kaduna. Mai shekara 23, ta kafa tarihi. Ta yi kokari wajen yaki da ’yan bindiga a shirin  Operation GAMA AIKI, Allah Ya ji kanta.

__________________________________________________________

ZAZKID | PR | BLOGGER @badmus_fazaz

Ina addu’ar Ubangiji ya sa Tolulope Arotile kin huta, sannan ya bai wa ’yan uwanki juriyar rashin jarumar mace.

_________________________________________________________

“Rashin Tolulope Arotile ta bar babban gibi a ci gaban Najeriya. Duk kalaman da zan fada ba za su dawo da ke ba a raye. Ina godiya da irin hidimar da kika yi wa Najeriya. Allah Ya jikanki”, inji Adewale A. Majofodun @Adewale_Majoff

“Duniya  ke nan, watanni kadan da suka gabata muke mika sakon taya murna, amma yanzu rai ya yi halinsa”, a cewar Auntee Rita @mamacitatweet.

Somto Okonkwo @MrSomtoOkonkwo ya wallafa cewa ’Yar Najeriya matukiyar jirgin sama ta farko Tolulope Arotile ta mutu…Ta rasu ta nada shekara 23 kacal. Kin mutu kina da matashiya Tolulope, wannan ya zo ne kamar mafarki.

Nicky Baby @Nickybaby kuma ta ce “yanzu nake samun labarin mutuwar ba-zata na mutuwar matukiyar jirgin sama Tolulope Arotile (Mace ta farko marukiyar jirgin yaki ’yar Najeriya) ta rasu a hatsarin mota muna yi mata addu’ar samun nasara”.

Shi kuma Peter Dumkwu @Peter_Dumkwu ya ce “Mutuwa ta dauke rayukan jama’a da dama da ba a yi zato ba a wannan shekarar. Allah Ya ji kan ki. Shi kadai Ya san dalilin rasuwarki.

Yung denzL @MI_Abaga, ya ce Allah Ya jikan Tolulope Arotile. Jarumar ‘yar Najeriya da ta fara tuka jirgin yaki ‘yar shekara 23!!!! Ba za mu manta ki ba”.