✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

CBN zai tallafa wa manoman tumatir a Kano

Babban Bankin Najeriya CBN) ya ce, kwanan zai kaddamar da shirin bayar da tallafin kudi ga manoma tumatir a Jihar Kano da sauran manoma tumatir…

Babban Bankin Najeriya CBN) ya ce, kwanan zai kaddamar da shirin bayar da tallafin kudi ga manoma tumatir a Jihar Kano da sauran manoma tumatir da ke sauran sassan kasar.

A cewar Bankin CBN hakan zai bunkasa noman tumatir a kasar nan da rage shigo da tumatirin gwangwani daga kasashen waje.

Mai ba Gwamnan Bankin CBN Shawara na Musamman a Fannin Bunkasa Kudade, Mista Anthony Efechikwu ne ya tabbatar da haka lokacin wakilan bankin suka ziyarci Kamfanin Tumatir na Dangote da ke Kadawa a Jihar Kano.

Mista Anthony ya ce, ayarinsu ya ziyarci kamfanin tumaturin ne don tantance matakan da za a bi a kara wa manoman tumatir kwarin gwiwa da bunkasa harkar noman tumatir.

Mista Anthony, ya kara da cewa, Bankin CBN na ci gaba da zuba kudade wajen bunkasa noman tumatir da kara darajarsa a Najeriya.

Bankin CBN zai yi aiki tare da kungiyoyin manoma tumatir wajen bai wa manoman tallafin kudi kamar yadda suke bukata.

Manajan Daraktan Kamfanin Tumatir na Dangote Malam Abdulkareem Kaita, ya ce kamfanin ya fara aiki da tan 1,200 na tumatir a kullum, wannan ba shi ne yawan adadin da kamfanin zai rika ci gaba da sarrafawa ba, kamfanin ya shirya abubuwa da dama wajen tabbatar da an tallafa wa manoman tumatir a yankin.