✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Chelsea ta daukaka kara ga FIFA

Kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea da ke Ingila ta daukaka kara ga Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, (FIFA) kan dakatar da ita daga sayen matasan…

Kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea da ke Ingila ta daukaka kara ga Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, (FIFA) kan dakatar da ita daga sayen matasan ’yan kwallon kafa.

A makon jiya ne Hukumar FIFA ta dakatar da Chelsea daga sayen sababbin ’yan wasa, saboda karya dokokin daukar matasan ’yan wasa da kungiyar ta yi.

Hukumar ta ce an karya doka a kan sayen ’yan wasa 29 daga cikin 92 da kungiyar ta dauka.

Haramcin wanda zai kai har zuwa karshen watan Janairun 2020, ba zai hana Chelsea sayar da nata ’yan wasan ba.

Kuma ba zai shafi kungiyar mata ta kulob din da kuma ta kwallon kafar Futsal ba, wato masu taka leda a rufaffen daki.

Haka kuma FIFA, ta ci tarar kungiyar Fam dubu 460, (kimanin Naira miliyan 216 da dubu 660), inda kuma Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila (FA) aka ci ta tarar Fam dubu 390 (kimanin  Naira miliyan 183 da dubu 890).

Haramcin ya zo ne bayan wani bincike da FIFA ta yi a kan wadansu matasan ’yan kwallo da Chelsea ta saya, har da tsohon dan wasan gabanta Bertrand Traore.