Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Chelsea ta fara zawarcin Isco

Rahotanni da ke fitowa daga kulob din Real Madrid na Sifen sun ce dan kwallon gaba a kulob din Isco yana yunkurin barin kulob din a watan gobe idan aka bude kasuwar cinikin ’yan kwallo.

Kulob da dama ne suke zawarcinsa, ciki har da Chelsea da na Manchester City a Ingila.  Amma alamu sun nuna Chelsea ce ta fi zakewa don ganin ta dauke dan kwallon.

ADVERTISEMENT

Rahotanni sun ce Chelsea ta taya dan kwallon a kan Fam miliyan 70 (kimanin Naira biliyan 33) kuma tana sa ran biyansa albashin Fam dubu 250 (kimanin Naira miliyan 117) a kowane mako.

Jaridar  The Sun ta Ingila ta ce, Isco wanda wasanni 11 kacal ya buga wa kungiyar Real Madrid a gasar La-Liga ta bana, ya zaku ya bar kulob din a watan Janairu ganin yadda yake yawan zama a benci.

ADVERTISEMENT

A ranar da kulob din CSKA Mosko ya doke Madrid da ci 3-0 a gasar Zakarun Turai magoya bayan Madrid sun rika yi masa ihu, al’amarin da ya sa ya yanke shawarar barin kulob din.