Search
Subscribe
China ta rusa kaburburan Musulmin Uighur

China ta rusa kaburburan Musulmin Uighur

Kasar China ta rusa makabartun al’ummar Musulmin kabilar Uighur, inda ta tono kasusuwan matattun da aka binne shekaru aru-aru, abin da masu kare hakkin dan Adam suka bayyana da yunkurin shafe duk wata alama da ke nuna wanzuwar wannan kabila a yankin Dinjiang.

Wani bincike da Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP) ya gudanar ta hanyar amfani da tauraron dan Adam, ya nuna cewa, a cikin shekaru an rusa gomman makabartun al’ummar a yankin Arewa maso Yammacin kasar.

’Yan jaridar AFP sun gane wa idanunsu yadda aka tono kasusuwan matattun, sannan aka watsar da su tamkar shara, yayin da aka shafe kaburburansu ba tare da nuna kula ba.

’Yan kabilar Uighur da ke rayuwa a kasashen ketare, sun ce, wannan rusau, wani bangare ne na shirin gwamnatin kasar don ganin ta murkushe tsirarun ’ya’yan kabilar.

Salih Hudayar, daya daga cikin jama’ar Uighur, ya ce, China na son shafe duk wani abu da ke alamta tarihinsu a kasar, yana mai cewa, an rusa kaburburan da aka binne kakannin-kakanninsa.

Gwamnatin China ta tsare akalla Musulmin Uighur miliyan daya a sansanin wanke kwakwalwa da ke Dinjiang da zimmar yaki da tsattsauriyar ra’ayin addini, yayin da take ci gaba da sanya ido sosai kan ’yan kabilar da ba a killace su ba.

Kazalika kasar ta haramta wa matan Uighur sanya hijabi kamar yadda ta haramta wa mazansu ajiye gemu.

Kasar China ta ci gaba da yin kunnen kashi duk da sukar da take sha daga kasashen duniya kan yadda take azabtar da Musulmi ’yan kabilar Uighur. Ko a wannan mako, sai da Amurka ta yi barazanar hana bizar tafiye-tafiye ga hukumomin kasar saboda cin zarafin jama’ar Musulmin.

A can baya, rahotanni sun ce, an rusa masallatan da ’yan kabilar ke gudanar da ibadunsu.

Kodayake hukumomin China sun fake da cewa, ayyukan raya birane ne dalilan da suka sa ta dauki matakin na rusau.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin