✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

China ta tura sojoji iyakar Hong-Kong

Shugaban Amurka Mista Donald Trump, ya ce kasar China ta soma girke sojoji a kan iyakarta da Hong-Kong inda zanga-zangar neman sauyi ke ci gaba…

Shugaban Amurka Mista Donald Trump, ya ce kasar China ta soma girke sojoji a kan iyakarta da Hong-Kong inda zanga-zangar neman sauyi ke ci gaba da yin kamari.

Shugaba Trump ya sanar da haka ne a wani sako ta kafar Twitter, inda ya yi kira ga bangarorin da ke rikici a Hong-Kong su bi hanyar lalama wajen warware rikicin. Ya bayyana fatar ganin ba a sake kashe ko mutum guda a rikicin a nan gaba ba.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ’yan sandan kwantar da tarzoma a Hong-Kong suka yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zangar neman sauyi da ke zaman dirshan a filin jiragen saman birnin.

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP) ya ruwaito cewa ’yan sandan sun yi amfani da barkonon tsohuwa domin tsira daga kofar ragon da wadansu daruruwan masu zanga-zangar suka yi wa motarsu da ke rakiyar wata motar asibiti.

’Yan sandan sun kuma kama akalla mutum biyu daga cikin masu zanga-zangar wadanda ke ci gaba da dagula harkokin sufuri a filin jirgin saman birnin Hong-Kong.

A tsakiyar makon nan, tashar talabijin ta Aljazeera ta bayar da rahoton cewa masu zanga-zangar sun kutsa cikin filin jiragen saman Hong Kong, lamarin da ya haifar da katse tashi da saukar jirage na wani lokaci,  wanda ya shafi jiragen da ke tashi zuwa kasa da kasa. Sai dai masana sun ce hakan ba zai gurgunta tattalin arzikin Hong-Kong ba.

Daga baya an bude tashar, bayan wani mummunan dauki-ba-dadi a daren Laraba, tsakanin masu zaman dirshan da jami’an tsaro, wadanda suka ce sun samu umarnin wata kotu da su fitar da masu zaman dirshan daga filin jiragen saman da karfin tuwo.

A wata hira da tashar talabijin din Aljazeera, wani kwararre a kan kasar China, Gordon Chang, ya ce hanya guda da China za ta yi amfani da ita wajen kawo karshen zanga-zangar, ita ce ta tursasa wa Shugabar yankin Hong Kong, Carrie Lam, ta yi murabus.

Miliyoyin masu zanga-zanga dai sun shafe mako 10 suna jerin gwanon neman a dawo da wasu hakkoki da kuma ’yancin dan Adam a yankin na Hong Kong, wanda ya zama kalubale mafi girma da China ta taba fuskanta a ikon da take yi wa yankin na Hong Kong mai kwarya-kwaryan ’yanci,  bayan mika mata shi da Birtaniya ta yi a 1997.