✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ci gaban siyasata ta dogara ga Ganduje – Doguwa

Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Wakilai, Alhaji Alhassan Ado Doguwa ya ce ci gaban siyasarsa ya ta’allaka ne ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje. Alhassan Ado…

Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Wakilai, Alhaji Alhassan Ado Doguwa ya ce ci gaban siyasarsa ya ta’allaka ne ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje. Alhassan Ado Doguwa ya bayyana hakan ne lokacin da ya jagoranci dandazon jama’a daga Masarautar Rano, domin yin godiya ga Gwamna Ganduje a kan goyon bayan da ya ba shi ya samu mukamin Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Wakilai.

Doguwa ya ce  ba zai yi da-na-sani ba wajen yin alaka da Ganduje. Ya ce “Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi min komai a samun nasarata na zama Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Wakilai, ya tsaya min a duk wata gwagwarmaya na ganin an cimma wannan matsayi.” Ya kara da cewa Gwamnan shugaba ne da duk wanda ya yi alaka da shi ba zai yi da-na-sani ba.

Da yake maida jawabi Gwamna Abdullahi Ganduje ya ba da tabbacin ci gaba da bai wa Alhaji Alhassan Doguwa duk goyon bayan da yake bukata a harkokin siyasarsa. Ya ce “Zan iya tsaya masa  ya zama Shugaban Majalisar Wakilai inda da damar yin haka.”