✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cibiyar Cinikayya ta Kano ta shirya baje koli don shigowar Ramadan

A wannan makon ne Cibiyar Bunkasa Ciniki da Harkokin Masana’antu ta Jihar Kano  (KACCIMA) ta shirya wani kwarya-kwaryar baje kolin kayayyaki a dandalin baje koli…

A wannan makon ne Cibiyar Bunkasa Ciniki da Harkokin Masana’antu ta Jihar Kano  (KACCIMA) ta shirya wani kwarya-kwaryar baje kolin kayayyaki a dandalin baje koli na jihar da ke kan titin zuwa gidan namun daji saboda shigowar watan azumin Ramadan.
Baje kolin wanda shi ne karo na uku  a tarihin cibiyar, an fara shi ne a ranar Talatar da ta gabata,  kuma za a dauki tsawon makonni biyu ana gudanar da shi.
Darakta Janar din cibiyar Ibrahim Tukur Barau ya shaida wa Aminiya cewa cibiyar tasu ta shirya wannan baje kolin ne domin nema wa talaka sauki game da yadda  farashin kayayyaki musammman kayan abinci ke tashin gwaron zabi a duk lokacin da watan azumin Ramadan ya gabato. “Mun shirya wannan baje koli ne domin lura da muka yi da irin yadda kayayyakin abinci ke tashi a duk lokacin da aka ce watan azumi ya karato, ga shi kuma abu ne mai matukar wahala ka tilasta wa dan kasuwa ya rage farashin kayayyakinsa, don haka muka ga dacewar mu gayyato ’yan kasuwar nan su zo su baje kolin kayansu a wannan wuri kyauta ba tare da biyan kudin haya ba, amma da sharadin su kuma za su rage farashin kayayyakinsu. Ban da kananan ’yan kasuwa, mun kuma samu kamfanoni irinsu dangote da Bua duk sun amsa tayinmu tare da yin alkawarin sayar da kayansu a kan farashin kamfani, ” Inji shi.
Alahaji Barau ya kara da cewa,  cibiyar ta kafa wani kwamiti da yake zagayawa wurin da ake gudanar da baje kolin domin tabbatar da cewa ‘yan kasuwar suna sayar da kayansu a kan farashin da ya kamata, wato ba su yi amfani da wannan damar wajen kara kudin kayayyakinsu ba.
Aminiya ta tattauna da Malam Aliyu dahiru Abdullahi, wani mai sayar da dankalin Turawa  a dandalin baje kolin inda ya bayyana cewa wannan abu da cibiyar ta bullo da shi abu ne da zai taimaka kwarai da gaske, musamman ma da yake su ma suna kwadayin samun ladan wannan wata mai alfarma, sannan a gefe daya kuma suna sayar da kayayyakinsu kan lokaci, “Baya ga lada da za mu samu bisa rage farashin da muka yi, a gefe guda kuma muna samun damar sayar da kayayyakinmu kan lokaci ba kamar yadda muka saba sayarwa a kasuwa ba, domin a kiyasi a kasuwa mukan sayar da buhun dankali biyu zuwa uku a rana, amma a nan wurin mukan sayar da buhu takwas zuwa goma a kullum.” Inji shi.  
Ita kuwa Malama Halima ta bayyana wa Aminiya yadda ta samu wannan baje kolin, inda ta ce ta samu kayayyakin abinci a farashi mai sauki idan aka kwatanta da yadda ake sayarwa a kasuwa, don haka ta roki gwamnati ta ci gaba da gudanar da irin wannan baje koli a duk shekara.
Shi kuwa Malam Abba Usman Muhamamd kira ya yi ga gwamnati cewa kamata ya yi nan gaba idan za a sake shirya irin wannan baje kolin ita gwamnatin da kanta ta dauki nauyin sayen kayayyakin abincin tare da rage farashin nasu, wanda hakan zai fi samar da saukin da ake tunani ga talaka fiye da idan kayayyakin suka zamo na ’yan kasuwa ne.
Aminiya ta gano cewa akwai saukin farshin kayayayyakin da ake sayarwa a wanann dandali na baje koli idan aka kwatanta da farshin kasuwa, misali karamin buhun dankai ana sayar da shi Naira 3000 a kasuwa yayin da ake sayar da shi a kan Naira 2,300 a filin baje kolin.