✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cibiyar TECKNOSAF ta horar da manoma dubu uku dabarun noma

Cibiyar nan dake tallafa wa rayuwar manoma domin bunkasa arzikinsu musamman ma manoman shinkafa da tumatir wacce aka fi sani da (TEKNOSAF) ta horar da…

Cibiyar nan dake tallafa wa rayuwar manoma domin bunkasa arzikinsu musamman ma manoman shinkafa da tumatir wacce aka fi sani da (TEKNOSAF) ta horar da manoman shinkafa 300 a Jihar Kano sabbin dabarun noma. Da yake jawabi a wajen taron horarwa wanda cibiyar ta gudanar a karamar Hukumar Warawa, Shugaban bunkasa noman shinkafa da tumatir na kungiyar anan Kano, Mista Olorinfemi Toyin ya jaddada aniyar kungiyar na tallafa wa manoma ba tare da karbar ko sisi daga hannunsu ba, tare kuma da tabbatarwa manoman sun sami ci gaba a harkar noman nasu.

A jawabinsa, Jami’in bayar da horo na cibiyar, Abdulrashid Hamisu Ibrahim a madadin shugaban shirin ya bayyana cewa makasudin taron shi ne don bunkasa noman shinkafa da tumatir a garin na Warawa da kuma Najeriya gaba daya “Domin mu nuna wa al’umma abin da muke yi wajen bunkasa harkar noman shinkafa da tumatir. Manoman za su fada da bakinsu game da abin da muka yi tun daga kan shuka har zuwa yanka.

Muna koya musu dabarun yadda za su inganta nomansu. Mu hada su da wuraren da za su sami kayayyakin noma masu inganci kamar su taki da iri da sauransu. Mu kuma sama masu kasuwanni don shigar da kayan amfanin gonar nasu. Sannan mu taimaka musu yadda za su hadu da bankuna wadanda za su ba su bashi da sauransu” Wasu manoma da suka amfana daga horarwar da cibiyar ta yi musu, sun bayyana farin cikinsu game da hakan.

Malam Amadu Maikano ya bayyana cewa “Mun karu da wannan kungiya domin ta nuna mana dabarun noma. Haka kuma sabanin sauran kungiyoyi wannan kungiya ba ta karbi ko anini a hannunmu ba da sunan kudin rajista ko wani abu makamancin hakan ba. Mu dai mun nuna mata gonakinmu ita kuma ta kawo iri ta nuna mana yadda za mu rika zuba shi a layi a maimakon watsa shi da muke yi ada, sun gaya mana cewa idan mun zuba iri a layi zai saukaka mana yin ciro da sa taki ba tare da an samu wata matsala ba. Sannan suka nuna  mana cewa idan mun zo dashe dai dai za mu yi a maimakon yadda muke yi a baya, inda muke dasa uku ko hudu. Alhamdulillahi da muka bi wadannan sabbin hanyoyi mun ga alherin hakan.”

Ita ma wata mai noman shinkafa, Habiba Garba ta bayyana cewa ta karu da wannan horarwar “Domin a baya da ka muke yin aiki, amma yanzu da zuwan wannan kungiya muna aiki ne bisa tsarin eke-eka” Taron dai ya sami halartar manoma daga garuruwan Wudil da Ajingi da kiru da karaye da wasu garuruwan dake jihar.