✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cikar Sarkin Jama’a shekara 20 a kan karaga (1)

A ranar Juma’ar da ta gabata ce Mai martaba Sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad II ya cika shekara 20 da hawa kujerar sarautar Jama’a,…

A ranar Juma’ar da ta gabata ce Mai martaba Sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad II ya cika shekara 20 da hawa kujerar sarautar Jama’a, kujerar da ya gada iyaye da kakanni, inda Sarkin ya shirya walima tare da addu’o’i a fadarsa.

Alhaji (Dokta) Muhammad Isa Muhammad (FICEN, OFR, CON) ya zama Sarkin Jama’a ne a ranar 23 ga watan Nuwamban 1998 bayan rasuwar mahaifinsa Alhaji Isa Muhammad Sani, wanda ya yi sarautar Jama’a daga1961 zuwa 1998. Wakilinmu ya waiwaya baya ya rubuta wani abu kan tarihin masarautar:

 

Takaitaccen tarihin Masarautar Jama’a

Kamar sauran masarautun Daular Usmaniyya, masarautar Jama’a, mai hedkwata a garin Kafanchan ta samo asali ne a sanadiyyar jihadin Shehu Usmanu Dan Fodiyo a 1804 inda dan Sarkin Kabin Yabo Muhammadu Moyijo, mai suna Malam Usman Yabo ya kafa masarautar ta Jama’a a 1810, a matsayinsa na daya daga cikin daliban Shehu Usmanu da aka tura wurare don karantarwa da kuma yada addinin Musulunci, kamar yadda Kuyambanan Jama’a, Alhaji Garba Maisukuni ya shaida wa Aminiya.

Kuyambanan, ya kara da cewa Malam Usman Kabin Yabo ya fara yada zango ne a Gundumar Kajuru kafin daga baya saboda wasu matsaloli da sarakunan lokacin da suka kai ga yunkurin hallaka shi, sai ya yi hijira zuwa kasar Sanga inda aka karbe shi tare da ba shi kariya daga mayakan da suka biyo bayansa daga Kajuru.

Sarki Usman Yabo, tare suka yi karatu wajen Shehu Usmanu da Malam Musa wanda daga baya ya zama Sarkin Zazzau na farko a Daular Usmaniyya.

Kabilun Sanga da suka hada da Numana da Ninzo da Ayu da kuma Hausawa da Fulani da suka zama kashin bayar kafa masarautar, a gefe daya da kuma wasu kabilu da suka hada da Kaninkon da Kagoma da Yeskwa da Gwandara sun kasance karkashin Masarautar Jama’a na tsawon shekara 180 kafin su samu masarautunsu daga baya wanda hakan, ya rage fadin kasar masarautar Jama’a wacce a yanzu take da shekara 208 da kafuwa.

Masarautar Jama’a a lokacin ta yi iyaka da masaurautun Keffi da Lafiya a Jihar Nasarawa, a Arewa maso Gabas kuma ta yi iyaka da Masarauta Zazzau.

Cibiyar masarautar Jama’a ta fara zama ne a yankin Sanga da ke Karamar Hukumar Sanga. Bayan karbo tuta daga Shehu Dan Fodiyo a 1810 sai Sarkin Jama’a na farko Usmanu Yabo ya yanke shawarar matsowa tsakiya don daidaita tafiyar da mulkinsa, inda hakan ta sa ya dawo da cibiyar masarautar zuwa Gidan Waya.

Wannan tashi ko hijira shi ne na farko da masarautar ta yi kafin ta sake yin kaura ko hijira na biyu daga Gidan Waya zuwa garin Madakiya a 1926. Bayan nan sai masarautar ta sake tasowa zuwa dajin da yanzu ake kira Kafanchan wanda a wancan lokacin wadansu Fulani da Hausawa ke zaune a dajin kuma dajin na karkashin masarautar ta Jama’a ce.

Kaurar da masarautar ta yi ya zo daidai da isowar titin jirgin kasa da aka dauko daga garin Fatakwal zuwa Kaduna inda suka iso daidai filin (Kafanchan).

Yayin da aka tambayi Sarki Muhammadu Sani  daidai inda za a kafa tashar jirgin sai ya ce, da su ku je ku “KAFA-A-CAN” yayin da ya yi musu ishara da dajin da yanzu ake kira KAFANCHAN daga KAFA-A-CAN.

Sarakunan Jama’a

Masarautar Jama’a ta yi Sarakuna 11 wadanda dukansu tushensu guda ne, ke nan babu batun gidajen sarauta sai dai dakunan sarauta a masarautar.

Bayan rasuwar Sarki Usman Yabo a 1833 sai dansa Abdullahi ya gaje shi sai kanensa Musa dan Usmanu ya gaje shi ya zama Sarki na uku. Bayan shi ne sai Sarki Adamu, sai Sarki Muhammadu Ada. Wadannan dukansu ’ya’yan Sarki Usman Yabo ne.

A 1883 ne Abdurrahman Maccido da aka fi sani da Sarki Machu ya zama Sarki na shida daga nan zai Sarki na bakwai Muhammadu dan Asama’u sai Sarki na takwas Abdullahi Maje Jos wanda a lokacinsa ne Turawan mulkin mallaka suka fara mulki kuma saboda sabanin da ya samu da su sai suka tsige shi suka tura shi Jos inda ya koma da wadansu jama’arsa suka kafa Unguwar Sarki a Jos.

Bayan tsige shi ne suka nada kanensa Malam Muhammadu Sani wanda shi ne kakan Sarkin Jama’a na yanzu. A lokacinsa ne hedkwatar masarautar ta dawo garin Madakiya wanda ya samo sunansa daga Madaki. (Madakiya yanzu tana karkashin Karamar Hukumar Zangon Kataf).

Bayan rasuwar Sarkin Jama’a Muhammadu Sani ne dansa Alhaji Isa Muhammad ya zama Sarki na 10 inda ya yi sarauta daga 1961 zuwa 1998.

Kamar kowace masarauta da ke Arewacin Najeriya, Masarautar Jama’a na da sarautu daban-daban. Daga cikin sarautun da suka kebanci ’ya’yan Sarki a masarautar ta Jama’a akwai; Magajin Gari da Dan Galadima da Dan Madami da Barade da Ciroma da Yarima da Uban Doma da Sarkin Fada da Iya da sauransu.

A Masarautar Jama’a akwai Sarkin kabilar Ibo da Sarkin Yarbawa da Sarkin Kabilu.

Ga jerin jadawalin Sarakunan Jama’a da shekarun da suka yi a kan mulki.

1 – Malam Usman Yabo 1810 – 1833

2 – Sarki Abdullahi 1833 – 1837

3 – Sarki Musa 1837 – 1850

4 – Sarki Adamu 1850 – 1869

5 – Sarki Muhammadu Ada 1869 – 1881

6 – Sarki Abdurrahman Maccido 1881 – 1911

7 – Sarki Muhammadu Dan Asma’u 1911 – 1915

8 – Sarki Abdullahi Maje Jos 1915 – 1926

9 – Sarki Muhammadu Sani 1926 – 1960

10 – Alhaji Isa Muhammad 1961 – 1998

11 – Alhaji Muhammad Isa Muhammad 1998 – zuwa yau.