Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Cikin hotuna: Yadda aka yi Babbar Sallah a Najeriya

Cikin hotuna: Yadda aka yi Babbar Sallah a Najeriya

Ga wasu kayatattun hotunan ranar Babbar Sallah daga sassan Najeriya.

Masallata sun yi ruku’u a lokaci sallar idi a Maiduguri, Jihar Borno.
Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero a ranar sallah, tare da ‘yan majalisarsa.
Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila ya jagoranci iyalan gidansa sallar idi a gida.
Gwamnan Borno, Babagana Zuluma tare da tsohon gwamna, Kashim Shettima a filin idi a Maiduguri.
Yadda mata suka yi sahu gabanin a tayar da sallah a filin idi na Sultan Bello, Kaduna.
Ministan fasahar sadarwa, Isa Ali Pantami yana gyaran kayan cikin ragon layya.
Tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II tare da iyalansa a ranar Sallah.
Sahun maza a filin idi na Sultan Bello suna jiran isowar liman kafin a tayar da sallah.
‘Yan kasuwa sun baje hajojinsu a kan titin da ke makwabtaka da filin idi na Sultan Bello.
Shugaba Buhari da jami’an gwamnatinsa suna bin limamin Fadar Shugaban Kasa sallar Idi.
Babban Limamin Ilori, Dakta Muhammad Bashir Imam-Soliu, yana gabatar da hudubar Idi
Masallata na sauraron huduba daga Shaikh Muhammad Sulaiman bayan idar da sallah a filin idi na Sultan Bello.
Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila a lokacin da zai yanka ragon layyarsa.
Shugaba Buhari tare da iyalansa bayan saukowa daga idi a Fadar Shugaban Kasa.
Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris filin idi na Kofar Doka, Zariya.