Da Dumi Dumi

Cikin kwanaki 100 gwamnatinmu ta yi  rawar gani a Bauchi – Kakakin PDP

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad

Kakakin Jam’iyyar PDP na jihar Bauchi Alhaji Yayanuwa Zainabari ya bayyana cewa cikin Kwanaki dari da kama mulkin Jamiyyar PDP a Jihar Bauchi Gwamnan Jihar Sanata Bala Muhammad Abdulkadir ya yi rawan gani bisa ire iren ayyukan raya kasa da zasu kyautata rayuwar al’ummar birni da karkara.

Zainabari ya bayyana hakane lokacin da yake zantawa da manema labarai a Bauchi Yace Jihar Bauchi ta sha wahala a shekaru hudu da suka wuce wajen gwamnatin APC tun da munyi alkawarin zamu yi wa alummar jihar aiki, tilas a samo mutane kwararru a fagagen da suka kware, kuma a nemo nagartattun mutane da bazasu baiwa gwamnati kunya ba, a kuma samu mutane masu dattako da kishin jama’ar Jiharsu.

Lokacin da yafara mulki Mai girma gwamna anyi shawarwari da masu ruwa da tsaki daga kowacce karamar hukuma an zakulo mutuum daya (1) da za a nada kwamishina kuma an kaiwa Majalisa, kuma majalisa ta sanar da cewa ta karbesu.

Zainabari yace kaga daga zuwan gwamna bai bata lokaci ba ya kaddamar da ayyukan Hanyoyi da kuma gyara sabbin hanyoyi a dukkan mazabun sanatoci guda uku dake Bauchi

Daga farko acikin garin Bauchi aka bada ayyukan hanyoyi guda hudu da suka hada da wadda ta tashi daga Ibrahim Bako ta fada kan hanyar zuwa Maiduguri, sai kuma hanyar da ta tashi daga Sabon Kaura zuwa Baban Titin Jos sannan aka bada ayyukan gyaran hanyoyin na MudaLawal dana rukunin gidajen dake Unguwar Yakubun Bauchi.

ADVERTISEMENT

Kakakin yace ba kawai kaddamar da ayyukan hanyoyin aka yi ba har ma an bada  kashi 50 na kudin aikin, kuma tuni aka nada shugabannin kananan hukumomi 20 an kuma tura sunayen kwamishinoni ga majalisar dokoki domin amincewa, kuma mafi yawa daga cikin wadanda za a nada gogaggun mutane da kowanne dan jihar Bauchi yasan kimarsu da jajircerwarsu wajen yin ayyukan raya kasa.

Share