✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cin zarafin Hakimi: Hukumar Abuja ta rushe shaguna a Mpape

Hukumar Kula da Gine-Gine ta Birnin Tarayya Abuja ta rusa shaguna da wasu gine-gine da ake zargin an yi su ba bisa ka’ida ba a…

Hukumar Kula da Gine-Gine ta Birnin Tarayya Abuja ta rusa shaguna da wasu gine-gine da ake zargin an yi su ba bisa ka’ida ba a garin Mpape, Abuja.

Ayarin hukumar wanda ya samu rakiyar jami’an tsaro ya gudanar da aikin ne a shekaranjiya Laraba da inda aka rusa shaguna da wani babban shagon zamani (plaza) da ba  a karasa su ba da adadinsu ya kai 40.

Aminiya ta ruwaito cewa shagunan dai wasu ’yan asalin garin ne suka gina a kan wani fili da wani kamfani fasa duwatsu ya bar ganimarsa a garin, bayan sauya matsuguni.

Hakimin Mpape Alhaji Abubakar Gimba wanda a baya ya nuna rashin goyon bayansa kan gina shagunan, saboda wajen na wucin gadi ne da gwamnati za ta iya bukata a kowane lokaci ya fuskanci cin zarafi daga wajen wadansu matasa a kan haka.

Matasan wadanda suka halarci zaman sulhu da Hakimin ya shirya kan maganar a fadarsa sun kai ga marinsa tare da cinna wa fadarsa wuta bisa zargin ya fifita ’yan kasuwar Fanteka da ke amfani da wajen a kan su ’yan asalin garin.

Wannan mataki na rusa wajen da hukumar ta yi a bangaren wadanda suka gina shagunan ana ganin, tamkar sakayya ce ga ’yan Fantekar wadanda a baya wata hukumar ta daban ta kona musu kayansu na sayarwa bayan kai samame a wajen bisa gayyatar ’yan asalin garin kamar yadda aka yi zargi.