✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ciyar da daliban firamare da ake yi daukar alhaki ne

Tsarin ciyar da daliban firamare a jihohi 26 na kasar nan da Gwamnatin Tarayya ke yi yana ci gaba da gudana, sai dai kuma tsarin…

Tsarin ciyar da daliban firamare a jihohi 26 na kasar nan da Gwamnatin Tarayya ke yi yana ci gaba da gudana, sai dai kuma tsarin yana tattare da matsalolin da sula kamata gwamnati ta duba da kyau domin cimma burinta na inganta harkar ilimi a fadin kasar nan.

Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da tsarin ciyar da daliban firamare ne a shekarar 2004, inda ta yi nufin farawa da jihohi 12 da kuma Abuja, amma bayan an fara da jihohi 10 da Abuja sai shirin ya rushe, jihohin Kano da Osun ne kawai suka ci gaba da tsarin.

A shekarar 2016 bayan gwamnatin APC ta shigo sai Gwamnan Jihar Kaduna ya rungumi tsarin, daga nan Gwamnatin Tarayya ita ma ta sake nanata niyyarta ta sake rungumar tsarin a shekarar 2016 inda ta yi hasashen za ta rika ciyar da daliban firamare miliyan 12 da dubu 800.

Kamar yadda Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya bayyana a yayin da yake jawabi a wani taro a Tunis na kasar Tunisiya, ya ce Gwamnatin Tarayya ta kashe fiye da Dalar Amurka miliyan 183 kuma dalibai miliyan 9 da dubu 300 da 892 da ke makarantun firamare dubu 49 da 837 a jihohi 26 ne suke amfana da shirin.

Haka kuma Mataimakin Shugaban Kasar ya ce, shirin ya samar da aiki ga masu girka abinci dubu 95 da 422 kuma fiye da kananan manoma dubu 100 ne suke samar da abubuwan da ake dafawa, kamar kayan abinci da kayan miya da kwai da sauransu.

Ya ci gaba da bayanin cewa a duk mako ana yanka shanu 594 da kaji dubu 138 kuma ana sarrafa kwai miliyan 6 da dubu 800 da tan 83 na kifi.

Babu shakka shirin ya taimaka kwarai wajen jawo hankalin yara su rika zuwa makaranta, domin sakamakon fito da shirin yara da yawa da suka kaurace wa makaranta sun koma, haka kuma an samu sababbin dalibai da yawa da suka shiga makaranta.

Haka kuma shirin ya bunkasa tattalin arzikin manoma da dama saboda kasuwa ta bude musu sakamakon sayen kayan abinci da masu girka wa dalibai abinci suke yi. Sannan ya samar da aiki ga masu dafa abincin, kuma shirin ya kara yawan kudin da ake juyawa a hannun jama’a.

Sai dai kuma ga alamu ba a nan gizo ke sakar ba, domin kuwa har yanzu harkar ilimi ba ta bunkasa ba a makarantun, saboda an bar jaki ne an koma ana dukan taiki.

Da farko dai a tsarin ciyarwar ba duka daliban makarantar ake ciyarwa ba, a makaranta a kan ware wadansu dalibai ne ake ba su abinci sauran dalibai kuma suna kallo, kuma abinci ba ya da ingancin da ake magana, a wasu makarantun ma a cikin leda ake zuba wa dalibai abincin. Ana zargin cewa ana cuwa-cuwa sosai a harkar ciyarwar inda maimakon a taimaka wa daliban sai ya kasance wata kafa ce aka samar wa wadansu domin su azurta kansu. Su kansu masu dafa abincin suna kukan cewa ba a biyansu kudinsu yadda ya kamata kuma ba a biya a kan lokaci.

Ta yaya za a samu ingantaccen ilimi a makaranta domin kawai an bai wa wadansu dalibai ’yan tsiraru abinci an bar sauran dalibai suna hamma, su kuma malamai ba a biyansu wani abin kirki, sannan ba a kula da sauran hakkokinsu?

Haka kuma an bar makarantun babu kayan koyarwa masu inganci, dalibai na zaune a kasa, gine-ginen makarantun sun lalace, babu rufi, ko babu tagogi da sauransu.

Maimakon kashe makudan kudi wajen ciyar da dalibai kamata ya yi gwamnati ta mayar da hankali wajen kyautata wa malamai da samar da wuraren karatu masu inganci da kayan karatu da na koyarwa na zamani.

Yin haka zai fi jawo hankalin yara su rika zuwa makaranta su zauna su yi karatu saboda kayan da ke makarantun za su rika jawo hankalinsu su zauna a makarantun, kayan wasannin yara irin kwallo da lilo da sauransu da kuma kayan karatu na zamani irin su kwamfuta, duk abubuwa ne da za su jawo ra’ayin yara su rika zuwa makaranta.

Amma ciyarwar da ake yi na wadansu dalibai a bar wadansu ba ta taimaka wa karatun dalibai, hasali ma dai wadansu dalibai da dama suna zuwa makarantar ne domin su ci abincin, da zarar sun ci sai su bar makarantar ba za su tsaya a ci gaba da karatu da su har a tashi ba.

Saboda haka lallai a sake duba wannan harka ta ciyar da dalibai abinci domin tsarin yana tattare da matsaloli kuma kwalliya ba ta biyan kudin sabulu duk da dimbin kudin da ake kashewa.

Idan har ya zama dole sai an ci gaba da ciyar da daliban firamaren to a rika ciyar da kowane dalibi, maimakon dauki dai-dai da ake yi a halin yanzu, inda ake ba wadansu abinci suna ci wadansu kuma suna kallonsu, domin wannan daukar alhaki ne.