✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Ciyar da daliban Kano kan lakume N4bn duk shekara’

Gwamnatin jihar Kano ta ce tana kashe zunzurutun kudi har Naira Biliyan hudu wajen ciyar da daliban jihar duk shekara.

Gwamnatin jihar Kano ta ce tana kashe zunzurutun kudi har Naira Biliyan hudu wajen ciyar da daliban jihar duk shekara.

Kwamishinan Ilimin jihar, Muhammad Sunusi Kiru shine ya tabbatar da hakan yayin wata tattaunawa kan nasarar ma’aikatar ilimin jihar cikin watanni 12 da suka gabata ga manema labarai.

Kiru ya ce, “Yanzu haka gwamnatin Kano ta samar da Kwalejin kimiyya ta tarayya a garin Ganduje dake karamar hukumar Dawakin Tofa.

“Mun kuma fara ginin katangar tare da manyan gini guda biyu mai dauke da azuzuwa guda shiga, sannan an basu kyautar mota sabuwa mai kujeru 32 domin jigilar dalibai, sai kuma mota kirar Hilux domin fara gudanar da al’amuran karatu,” cewar Kiru.

Kwamishinan ya kara da cewa sabbin makarantun da ake ginawa a dukkanin fadin sabbin masarautu biyar dake jihar sun kusa kammala.

A cewarsa, gwamantin jihar ta fi ba harkar ilimi muhimmanci fiye da komai, yana mai cewa ko a kwanan na ta ta fitar da kudade har Naira miliyan 107 ga daliban jihar dake karatu a Jamhuniyar Nijar.

Kiru ya kuma ce an fitar da Miliyan 93 a matsayin kudin abincin daliban Kano dake karatu a Kwalejin Harsuna dake Niamey a Jamhuniyar ta Nijar.