✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronabirus: China ta kori manyan jami’ai daga aiki

Kasa China ta kori manyan jami’anta daga mukamansu saboda yadda suka gaza magance barkewar cutar  numfashi ta Coronabirus yayin da alkaluman wadanda suka mutu suka…

Kasa China ta kori manyan jami’anta daga mukamansu saboda yadda suka gaza magance barkewar cutar  numfashi ta Coronabirus yayin da alkaluman wadanda suka mutu suka zarce 1,000.

Babban Sakataren Jam’iyyar Kwaminisanci a Hukumar Lafiya ta Lardin Hubei da Shugaban Hukumar na cikin wadanda suka rasa mukamansu.

Su ne manyan jami’an da kawo yanzu suka rasa ayyukansu, amma a baya an kori wadansu ma’aikata a matakai daban-daban.

Mataimakin Shugaban Kungiyar Agaji ta Red Cross a birnin ma ya rasa aikinsa saboda “watsi da aiki” kan yadda ake karbar kudade da kayan agaji.

A farkon makon nan, mutum 103 suka rasu a Lardin Hubei kawai, wanda wannan ne adadi mafi yawa tun da annobar ta barke a China.

Zuwa ranar Talata mutum 1,016 ne suka rasu a fadin kasar. Amma an samu raguwar wadanda suka kamu da cutar da kimanin kashi 20 cikin 100 idan aka kwatanta da ranar Lahadi, daga 3,062 zuwa 2,478.

 

Babbar barazana ce ga duniya – WHO

Yaiyn da adadin mutanen da cutar Koruna ta kashe a China ya haura dubu daya, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargadi kan yadda cutar ta zama babbar barazana ga duniya baki daya.

Yayin taron Hukumar WHO a birnin Geneba bayan karuwar wadanda ke dauke da cutar a China da ci gaba da fantsamarta a sauran kasashen duniya, Hukumar WHO ta bayyana cutar ta Kurona wadda ta sauya mata suna zuwa Cobid-19 a matsayin babbar barazana ga duniya baki daya.

Taron na Hukumar WHO na zuwa ne a daidai lokacin da China ke karfafa matakan yaki da cutar da yanzu haka ta kama fiye da mutum dubu 42, ba ya ga yaduwarta a kasashe 25, inda a ranar Talatar nan aka samu rahoton rasuwar mutum 108.

A cewar Shugaban Hukumar WHO, Mista Tedros Adhanom Ghebreyesus, China ke da kashi 99 cikin 100 na cutar ta Korona matakin da ke nuna bukatar agajin da kasar ke yi.

Miliyoyin mutane ne mahukuntan China suka kulle a mabambantan birane don gudun yaduwar cutar, matakin da WHO ke cewa akwai tsananin bukatar agajin gaggawa.

Bayan matakin kasashe na hana safarar jiragensu zuwa China da kuma tantancewa kafin karbar bakin da suka iso daga China. Kamuwar dan Birtaniya guda da ya shafa wa mutum 11 cutar ta Kurona ba tare da ya ziyarci China ko ya yi mu’amala da wani da ya zo daga kasar ba, ya yi matukar tayar da hankali tare da raba tunanin masana kan ko wani nau’in cutar ne ke shirin barkewa a Turai.

Yanzu haka Japan na da mutum 135 da suka kamu da cutar Kurona yayin da a ranar Talata, aka kwashe fiye da mutum 100 daga wani dogon gini mai hawa 35 da ke dauke da fiye da mutum dubu uku, bayan gwaji ga wadansu mutum biyu da aka gano suna dauke da cutar a Hong Kong, inda dukkansu za su fuskanci gwaje-gwajen lafiya don gudun fantsamar cutar zuwa wasu sassa.

 

Ta haddasa barna ga tattalin arzikin China

A China yanzu haka jama’ar kasar na cike da fargabar rasa aikin yi duk da tabbacin da Shugaba Di Jin Ping ya bayar na hana korar ma’aikata. Annobar ta haifar da mummunar nakasu ga tattalin arzikin kasar; inda ta yi sanadiyyar muguwar faduwar hannayen jarin, da ba a ta taba gani ba a cikin shekara hudu.