✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Adadin wadanda suka kamu a Najeriya ya haura 10,000

Adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Najeriya ya haura 10,000, kamar yadda alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta NCDC suka…

Adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Najeriya ya haura 10,000, kamar yadda alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta NCDC suka nuna.

Wani sako da hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter ya nuna cewa zuwa tsakar daren 31 ga watan Mayu, jimillar wadanda gwaji ya tabbatar sun kamu da coronavirus sun kai 10,162.

Adadin ya ketare zuwa wannan mataki ne bayan da aka samu sabbin majinyata 307.

Daga cikin sabbin kamun dai 188 a jihar Legas suke, 44 a Yankin Babban Birnin Tarayya, 19 a jihar Ogun, 14 a jihar Kaduna, 12 a jihar Oyo.

Sai kuma jihar Bayelsa mai mutum tara, da Gombe mai mutum biyar.

Daga nan sai jihohin Kano da Delta masu mutum uku-uku,  da Imo da Ribas da Neja da Bauchi masu mutum bibbiyu, sai kuma Filato da Kwara masu mutum guda ko wacce.

Alkaluman sun kuma nuna cewa yawan mutanen da aka sallama bayan sun warke ya kai 3,007, yayin da wadanda suka riga mu gidan gaskiya suka kai  287.