✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Akwai yiwuwar sanya dokar hana fita a Legas- Sanwo-Olu

Da yammacin ranar Juma’a ne gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana cewa za a rufe jihar Legas a sanya dokar ta baci, inda za…

Da yammacin ranar Juma’a ne gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana cewa za a rufe jihar Legas a sanya dokar ta baci, inda za a hana shige da fice a daukacin jihar mutukar ana ci gaba da samun wadanda ke kamuwa da cutar coronavirus a jihar.

Ya ce, mutukar aka kai ga samun wani adadi na masu kamuwa da cutar a jihar za a rufe ta ruf a hana fita ko shiga jihar, gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya yi wa al’umar jihar jawabi kai tsaye ta kafar sadarwa a gidan gwamnatin jihar da ke Marina, inda ya ce zuwa yanzu an samu mutum 44 da ke dauke da cutar coronavirus a jihar Legas