✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Al’ummar jihar Legas sun fara zaman dirshen a gida

Al’ummar jihar Legas sun bi umarnin mahukunta a jihar, sun  fara zaman dirshen na kwanaki 14 a gida. Aminiya ta garzaya sassa daban-daban na birnin…

Al’ummar jihar Legas sun bi umarnin mahukunta a jihar, sun  fara zaman dirshen na kwanaki 14 a gida.

Aminiya ta garzaya sassa daban-daban na birnin na Legas inda a baya ke cike da hada-hadar jama’a sai dai a yau babu kowa, rumfunan kasuwanni sun kasance a rufe, haka mafiya yawan manyan hanyoyin birnin Legas sun kasance fayau babu abin hawa ba kamar a baya ba da akan sami cunkoso ko hada-hadar jama’a ba.

A daya bangaren jami’an tsaro ne ke kai komo domin tabbatar da ganin ana bin umarnin zama a gida sauda kafa, haka zalika a wasu sassan garin na Legas mahukunta na ci gaba da yin feshi domin kawar da annobar Coronavirus.