✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: An dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa

Hukumomi sun sanar da dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa na fasinja a Najeriya saboda cutar Coronavirus. Wannan ne bangare na baya-bayan nan da aka dakatar…

Hukumomi sun sanar da dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa na fasinja a Najeriya saboda cutar Coronavirus.

Wannan ne bangare na baya-bayan nan da aka dakatar da harkokinsa a jerin matakan da ake dauka don gudun yaduwa cutar ta Coronavirus a kasar.

Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Kasa ta Najeriya ce ta sanar da hakan a wata sanarwa mai dauke da sa-hannun mataimakin daraktanta mai kula da sashen hulda da jama’a, Yakubu Mahmood.

“Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) ta yanke shawarar dakatar da dukkanin zirga-zirgar jiragen kasa na fasinja daga ranar Litinin 23 ga watan Maris”, inji Yakubu Mahmood.

Jami’in ya kuma kara da cewa, “[An dauki wannan mataki ne] sakamakon rahoton da samu na barkewar annobar cutar Coronavirus”.

Rahotanni dai na nuna cewa an samu wani bawan a Abuja, babban birnin kasar, wanda ke dauke da cutar bayan dawowarsa daga Birtaniya.

Sanarwar dai ba ta fadi wa’adin dakatar da zirga-zirgar ba, ko da yake ta ce Hukumar ta NRC za ta yi bayani idan bukatar hakan ta taso.

Wannan lamari dai ka iya jefa mutanen da ke kai-kawo ta jirgin kasa, musamman a tsakanin Abuja da Kaduna, cikin wani yanayi na gaba kura baya sayaki.

Tun bayan da yanayin tsaro ya tabarbare a hanyar da ta hade biranen biyu ne dai mutane da dama, ciki har da manyan jami’an gwamnati da manyan jami’an tsaro, suka koma tafiya ta jirgin kasa.