✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: An gano majinyatan da ‘suka tsere’ a Borno

Gwamnatin jihar Borno ta kame daya daga ciki wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus da aka ce sun tsere, yayin dayar ta kai…

Gwamnatin jihar Borno ta kame daya daga ciki wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus da aka ce sun tsere, yayin dayar ta kai kanta cibiyar da ake killace majinyata.

An dai gano namijin ne a wani sansanin ’yan gudun hijira da ke Maiduguri.

A cewar shugaban kwamitin hana yaduwar cutar na jihar Borno, Umar Usman Kadafur, mutumin da ya tsere din yana cikin wadanda suka yi jana’izar wani mutum da ya rasu a dalilin kamuwa da cutar.

“Wanda aka kama din, an gwada shi aka gano ya kamu da cutar bayan halartar wata jana’iza a garin Biu; haka dai ya samu ya tsere zuwa sansanin ’yan gudun hijira na Bakassi da ke kan hanyar Damboa”, inji Kadafur.

Ya kara da cewa bayan mutumin ya isa sansanin yan gudun hijirar ya yi mu’amala da jama’a da kuma iyalansa da ke wurin.

Shi ma kwamishinan lafiya, kuma sakataren kwamitin, Dokta Salihu Kwaya-Bura, ya ce bayan samun bayanai a kan inda mutumin yake, nan take kwamitinsu ya hanzarta dauke shi daga sansanin zuwa cibiyar da ake killace masu fama da cutar.

Ita kuwa majinyaciya ta biyu da aka ce ta tsere ta kai kanta ne Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduduguri, inda aka ce jami’ai sun ba ta hakuri.

An bai wa matar hakuri ne saboda ta yi bayanin cewa babu wanda ya kira ta ya shaida mata sakamakon gwajin da aka yi mata.

Wata sanarwa mai dauke da sa-hannun kakakin kwamitin yaki da cutar coronavirus a jihar ta Borno, Isa Gusau, ta ambato shugaban kwamitin yana yabawa da matakin da matar ta dauka.

Da yake karin haske a kan sakamakon wasu da aka gwada, Dokta Kwaya-Bura ya ce an samu mutum 15 da aka gwada ba sa dauke da cutar, amma wasu mutum biyu da aka kawo cibiyar daga Dikwa sakamakonsu ya nuna sun kamu da ita.

Da maraicen Lahadi ne dai hukumomi a jihar ta Borno suka ba da sanarwa cewa wasu mutum biyu da aka yiwa gwaji aka tabbatar sun kamu da cutar sun shiga wasan buya saboda sun gudun zuwa inda ake killace majinyata.