✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: An hana motocin jigila shiga Kano

Gwamnatin Kano ta bayar da umarnin hana motocin bas masu jigilar fasinja daga wasu jihohin shiga Jihar. Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar, Kwamared Muhammad Garba,…

Gwamnatin Kano ta bayar da umarnin hana motocin bas masu jigilar fasinja daga wasu jihohin shiga Jihar.

Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar, Kwamared Muhammad Garba, shi ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai ta yake gudanarwa a halin yanzu.

A cewar Kwamishinan gwamnatin ta kuma yi kira ga ma’aikatan jihar da su daina zuwa wuraren ayyukansu na tsawon makonni biyu a kokarin ta na dakile cutar Coronavirus.

Gwamnatin Jihar ta Kano ta bayyana cewa, ma’aikatan da umarnin zama a gidan bai shafa ba sun hada da malaman jinya da ma’aikatan bayar da ruwan sha da kuma wasu daga cikin ‘yan jarida.

“Ma’aikatan lafiya da suka hada da nas-nas da sauran ma’aikatan asibiti.

Haka su ma ma’aikatan da ke bayar da ruwan sha, saboda ba mu so a ce an rasa ruwan sha a fadin jihar. Su ma maaikatan da ke aikin watsa labarai su ma wannan umarni bai shafe su ba.”

Har ila yau gwamnatin ta haramta shigowar motocin Safa-safa masu zirga-zirga a jihar duba da yadda suke cunkusa fasinjoji a cikin motocinsu duk a kokarin gwamnatin na dakille cutar Coronavirus.

A wani ci gaban kuma Gwamnatin Jihar Kano ta amince da biyan Naira miliyan 21 ga daliban da za su rubuta jarrabawar IJMB a Kwalejojin Share Fagen Shiga Jami’a ta CARS da kuma ta Rabi’u Musa Kwankwaso.

Haka kuma gwamnatin ta sanya hannu akan biyan Naira Miliyan 15 ga daliban da suka cancanta da za su rubuta jarrabawar WAEC da NECO a bana.