✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: An rufe Masallacin Kasa da ke Abuja

Hukumar gudanarwar Masallacin Kasa da ke Abuja ta sanar da dakatar da yin salloli biyar cikin jam’i, da sallar Juma’a, da ma gudanar wasu taruka…

Hukumar gudanarwar Masallacin Kasa da ke Abuja ta sanar da dakatar da yin salloli biyar cikin jam’i, da sallar Juma’a, da ma gudanar wasu taruka a masallacin a matsayin hanyar dakile yaduwar cutar Coronavirus da ta zama annoba a duk duniya.

Sanarwar ta fito ne daga Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) wadda Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III, ke jagoranta.

“A yunkurin kauce wa barazanar yaduwar cutar COVID-19, mahukuntan  masallacin sun yanke shawarar dakatar da yin salloli biyar cikin jam’i da sallar Juma’a, da wasu tarukan da ake gudanarwa a masallacin.”

Sanarwar ta kara da cewa an rufe duk shaguna da gidajen abincin da ke harabar masallacin daga ranar Litinin 23 ga watan Maris, 2020 har zuwa wani lokaci.

“Muna rokon Alllah Ya kare mu daga wannan mummunar annoba, sannan akwai bukatar yin addu’o’i don neman Allah Ya kawar da annobar”, inji sanarwar.

Tun a karshen makon da ya gabata ne dai wasu kungiyoyin addinin Musulunci suka rufe masallatansu na Juma’a, da nufin bin shawarar mahukunta cewa a kaurace wa gudanar da tarukan mutane fiye da 50.