✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: An sallami mutum 7 a Abuja

Bakwai daga cikin mutanen da aka killace suna jinya sakamakon kamuwa da cutar coronavirus a Abuja sun koma cikin iyalansu a ranar Talata. Hakan dai…

Bakwai daga cikin mutanen da aka killace suna jinya sakamakon kamuwa da cutar coronavirus a Abuja sun koma cikin iyalansu a ranar Talata.

Hakan dai ya biyo bayan sallamar su ne da cibiyar dake kula da su ta yi bayan ta tabbatar da cewa sun samu lafiya.

Mai taimakawa ministan Yankin Babban Birnin Tarayya a kan al’amuran yada labarai Malam Abubakar Sani ne ya tabbatar da hakan ga Aminiya ranar Laraba.

Ya ce an sallami mutum bakwai din ne da misalin qarfe 6.30 na yammacin Talata daga Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja da ke Gwagwalada inda a ke yi masu jinya.

Malam Abubakar Sani ya ce ba zai iya bayar da sunayen wadanda aka sallama ba saboda yin hakan ya saba doka.

Tun farko dai ministan Yankin Babban Birnin Tarayya Malam Muhammad Musa Bello ya sanar da shirin sallaman majinyatan ga ‘yan jarida a yayin rangadin wasu karin cibiyoyi biyu da aka ware don kulawa da wadanda suka harbu da cutar ta COVID-19 a yankin a ranar Talata.

Ministan, wanda ya yaba wa jami’an kiwon lafiya a bisa kokarin da suke yi, ya kuma bayyana fatan sallamar ragowar majinyata 39 da ya ce suna samun kulawar likitocin.

A baya dai wasu ‘yan Njaeriya sun yi ta nuna damuwa saboda ganin ana ta sallamar wadanda suka warke a wasu wuarare, amma a Yankin na Babban Birnin Tarayya shiru ake ji.