✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: An samu sabbin kamuwa 12

An tabbatar da samun karin mutum 12 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Laraba. Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ce…

An tabbatar da samun karin mutum 12 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Laraba.

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ce ta bayyana hakan a sako na baya-bayan nan da ta wallafa a shafinta na Twitter.

“An bayar da rahoton samun sabbin kamuwa da COVID-19 a Najeriya; tara a Jihar Osun, biyu a Jihar Edo, da kuma daya a Jihar Eikiti”.

Hakan dai ya sa yawan wadanda aka tabbatar sun kamu ya karu.

“Zuwa karfe 12.30 na ranar 1 ga watan Afrilu an tabbatar da mutum 151 sun kamu da COVID-19 a Najeriya.

“Daga cikin wannan adadi an sallami mutum tara, yayin wasu mutum biyu suka riga mu gidan gaskiya”, inji NCDC.

Abba Kyari na murmurewa —Kwamishinan Lafiya

Wadanda suka cancanci gwajin Coronavirus

A cikin sabbin kamun dai babu ko mutum guda a Jihar Legas da Yankin Babban Birnin Tarayya, yankunan da suka fi yawan wadanda aka tabbatar sun kamu, yayin da Jihar Osun ta sha gaban Oyo da mutum shida.