✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Ana neman wani ‘majinyaci’ ruwa a jallo a Zamfara

Mahukunta a jihar Zamfara na neman wani mutum da aka tabbatar ya kamu da cutar Coronavirus, wanda ya gudu ya ke kuma wasan buya da…

Mahukunta a jihar Zamfara na neman wani mutum da aka tabbatar ya kamu da cutar Coronavirus, wanda ya gudu ya ke kuma wasan buya da hukumomi.

Mutumin mai suna  Jamilu Shinkafi ya ‘gudu’ ne bayan da aka yi masa gwaji aka kuma tabbatar   da cutar a tare da shi.

Jamilu Shinkafi dan unguwar Damba ne da ke garin Gusau, amma yana zaune a Yankin Babban Birnin Tarayya  Abuja.

Bayan da ya dawo daga Abuja sai ya yi zaman shi a gida kuma ba shi da lafiya.

Hakazalika binciken da jami’an  Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) a jihar suka gudanar ya nuna cewa  mutumin ya yi tafiye-tafiye tsakanin biranen Abuja da Legas.

‘Yadda aka yi gwajin’

Ma’aikatan lafiya sun je gidan shi kuma suka dauki samfurin gwajin cutar daga jikin shi; ko da sakamakon gwajin ya fito sai suka neme shi amma babu  labarinsa, ya fara wasan buya da su – sun neme shi ta waya ya ki dauka, kamar yadda wani jami’in Hukumar ta NCDC ya bayyana.

Ya ce daga baya sun yi magana da mutumin ta wayar salular wani dan uwansa, kuma ya musanta cewa yana dauke da cutar, kuma an samu rahoton  ya tafi Abuja daga bisani kuma aka ce ya je  Kaduna da Katsina.

Mahukunta a jihar ta Zamfara  sun baza komar su domin kamo shi, inda suka  sanarwa ma’aikatar lafiya ta tarayya halin da ake ciki domin daukar mataki.

Kwamishinan lafiya na jihar ta Zamfara Dokta  Yahaya Muhammad Kanoma ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya kuma kara da cewa suna nan suna bin sawun mara lafiyar da nufin sake kamo shi domin a killace shi.

Ya ki killace kan shi

Ya ce a lokacin da suka dauki samfuri domin yi masa  gwajin cutar sun ba shi shawarar ya killace kansa, amma ko da sakamakon ya fito ya nuna yana dauke da cutar sai yaki daukar kiran wayarsu, nan da nan kuma aka neme shi aka rasa.

“Mun yi magana da shi ta wayar dan uwansa, mun fada masa halin da ake ciki da sakamakon gwajin domin ya kawo kansa, sai ya musanta haka, yana cewa shi ba ya dauke da cutar”, inji kwamishinan.

Gidan radiyon BBC Hausa ya yi hira da mutumin, wanda aka jiyo shi yana cewa shi bai yarda yana dauke da cutar coronavirus ba.

‘Ni typhoid ke damu na’

“Na san cewa ba ni da lafiya amma zazzabin typhoid ne yake damu na, domin na yi kwana goma ina fama an yi mun gwaji aka ce typhoid ne, an dade ana yi min magani, an yi min salala da tiriri da menene dai kuma Allah ya sa na samu sauki, domin kusan allura 18 aka yi min,” inji mara lafiyar.

Ya ce kusan duk maganganun da mahukunta suke yi a kan shi ba haka ba ne, kuma a shirye yake ya zauna da su, a fuskanci juna.

A wasu jihohin ma an ba da rahoton wasu da aka tabbatar sun kamu da cutar sun yi batan dabo.

A jihar Kano ma dai ana can ana neman wasu majinyata biyu da aka ce babu su babu labarinsu.