Da Dumi Dumi

Coronavirus: Atiku ya jajanta wa Abba Kyari

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya jajanta wa Shugaban Ma’aikata a Fadar Shugaban Kasa, Malam Abba Kyari, wanda aka tabbatar yana dauke da cutar Coronavirus.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya mika gaisuwarsa ne ga Malam Abba Kyari da iyalansa a shafinsa na Twitter, inda ya kara da addu’a: “Allah ya kare mu gabaki daya, kuma ya ba shi lafiya”.

Shi ma dai tsohon Mataimakin Shugaban Kasar dansa ya kamu da cutar, kamar yadda ya sanar a shafin nasa ranar Litinin.

An yi amanna cewa Malam Abba Kyari ya kamu da cutar ne sakamakon wata tafiyar aiki zuwa kasashen Jamus da Masar.

An ba da rahoton cewa bayan dawowarsa, babban jami’in ya gana da wasu kusoshi a gwamnati, ciki har da Shugaba Buhari, da Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, da wasu ministoci.

ADVERTISEMENT

Sai dai bayan wani gwaji da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta gudanar ya nuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari bay a dauke da cutar.

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya