✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Gwamnatin Najeriya ta rufe filayen jiragen sama

Hukumomi a Najeriya sun sanar da rufe dukkan filayen jiragen sama na kasar ga matafiya daga ƙasashen waje. Matakin dai zai fara aiki ne daga…

Hukumomi a Najeriya sun sanar da rufe dukkan filayen jiragen sama na kasar ga matafiya daga ƙasashen waje.

Matakin dai zai fara aiki ne daga ranar Litinin 23 ga watan Maris zuwa ranar Alhamis 23 ga watan Afrilu.

Babban Daraktan Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Sama ta Kasa (NCAA) Kyaftin Musa Nuhu, ne ya bayyana haka a wata wasika da ya aike wa kamfanonin jiragen sama na kasashen waje.

A baya dai an hana matafiya daga wasu ƙasashen duniya 13 shigowa kasar.

Cikakken rahoton na nan tafe.