Da Dumi Dumi

Coronavirus: Gwamnatin Neja ta dakatar da sallar Juma’a

Gwamnan Jihar Neja Abubakar Sani Bello
Gwamnan Jihar Neja Abubakar Sani Bello na cikin gwamnonin da suka killace kansu bayan sun yi mu'amala da mutanen da aka tabbatar suna dauke da Coronavirus

Gwamnatin Neja ta bayar da umarnin dakatar da tarukan ibada a dukkan masallatan Juma’ar jihar da nufin hana cutar Coronavirus yaduwa.

Hakan dai na nufin da wannan umarni na gwamnati ba za a gudanar da sallar Juma’a ba a fadin jihar.

Sanarwar dakatarwar ta fito ne daga Sakataren Gwamnatin Jihar, Ahmed Ibrahim Matane.

A cewarsa, wajibi ne gwamnati ta yi aiki kafada da kafada da shugabannin addini da sauran masu ruwa da tsaki don ganin an yi dukkan mai yiwuwa an hana cutar ta COVID-19 shiga jihar balle ta samu wurin zama.

Tun a makon jiya ne dai hukumomi a Najeriyar suka fara kira ko bayar da umarni ga al’ummominsu da su hakura da tarukan addini a masallatan Juma’a da majami’u don hana cutar yaduwa.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya