✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hudu cikin matafiyan Sakkwato da aka tsare a Oyo na da Coronavirus

Hudu cikin 11 na matafiyan jihar Sakkwato da aka tsare a jihar Oyo suna dauke da cutar coronavirus. A gwajin da aka yiwa matafiyan ya…

Hudu cikin 11 na matafiyan jihar Sakkwato da aka tsare a jihar Oyo suna dauke da cutar coronavirus.

A gwajin da aka yiwa matafiyan ya tabbatar da cewa hudu daga cikin 11 na dauke da cutar.

Babban jami’in kula da cutar na jihar Oyo Dakta Taiwo Ladipo, ne ya tabbatar wa jaridar Tribune hakan a ranar Talata, 5 ga watan Mayu.

Ya ce an killace mutum hudun a cibiyar killace masu dauke da cutar da ke Olodo.

A ranar Juma’a, 1 ga watan Mayu, jami’an ‘yan sanda suka kame matafiyan a yankin Asijere a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Akure, a jihar Ondo.

Hukumar ‘yan sandan ta tsare matafiyan a ofishinta na Gbagi a ranar Juma’a, bayan tsare su ne gwmanan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya ce baza a sake su zuwa Sakkwato ba, har sai an yi masu gwajin cutar.

Bayan tsare matafiyan na jihar Sakkwato ne da kwana guda aka yi masu gwajin cutar, inda sakamakon gwajin ya tabbatar hudu daga cikin su na dauke da cutar.

A kwanakin baya ma mahukunta a Legas sun tsare wasu matafiya 40 a cikin babbar motar shanu, wadanda suka yi yunkunrin shiga jihar bayan sun taso daga Arewacin Najeriya,

Masu fashin baki sun shaida cewa za a ci gaba da samun matafiya daga Arewa zuwa jihohin Legas da Ogun tun bayan da gwmanatin tarayya ta ayyana saukaka dokar kulle a jihohin.