✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Hukumar jiragen kasa ta lashe amanta

Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) ta yi amai ta lashe, bayan da ta jingine shawarar da ta yanke ta dakatar da zirga-zirgar…

Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) ta yi amai ta lashe, bayan da ta jingine shawarar da ta yanke ta dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa na fasinja.

Wani sako da mai magana da yawun hukumar, Yakub Mahmood, ya aike wa wakilin Daily Trust ya ce an sauya shawarar ne da sharadi.

“Hukumar gudanarwa [ta NRC] ta yi nazari a kan lamarin ta kuma yanke shawarar ci gaba da zirga-zirga a bisa wasu sharudda”.

Wadannan sharudda, a cewar sakon, su ne: fasinjoji za su bayar da cikakkun sunayensu, da adireshinsu, da ranar haihuwarsu, da kuma wani katin shaida.

Tun da farko dai hukumar ta bayar da sanarwar dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa na fasinja a fadin Najeriya ne da nufin kauce wa yaduwar cutar Corona virus.

Wata sanarwa da Yakub Mahmood din ya sanyawa hannu ranar Asabar ta ce za a dakatar da zirga-zirgar ne daga ranar 23 ga watan Maris zuwa ranar 23 ga watan Afrilu.

Alamu dai na nuna cewa wasu masu fada-a-ji a Najeriya da ke amfani da jirgin kasa a tsakanin Abuja da Kaduna ne suka matsa wa hukumar lamba ta sauya shawara.

Wata majiya ta ce “An ja hankalin NRC cewa dakatar da daukacin jiragen kasa na fasinja ciki har da masu zirga-zirga a tsakanin Abuja da Kaduna ba abu ne mai kyau ba, idan aka yi la’akari da yanayin tsaro a kan hanyar mota”.

Babu wani bayani a kan ko jingine shawarar dakatar da jiragen na kasa ya shafi masu zirga-zirga tsakanin Abuja da Kaduna ne kawai ko kuma a duk fadin Najeriya ne.

Sakamakon tabarbarewar tsaro a hanyoyin mota a Najeriya dai, mutane da dama masu tafiye-tafiye a tsakanin Abuja da Kaduna, ciki har da manyan jami’an gwamnati da manyan jami’an tsaro, sun koma bin jirgin kasa.

Wannan ne ya sa a wasu lokutan wasu fasinjojin a tsaye suke tafiyar ta tsawon kusan sa’a biyu saboda yawan mutanen da ke bukatar shiga  ya fi yawan taragan jirgin.