✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Kano ta mayar da daliban musaya zuwa jihohinsu

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ta mayar da daliban musaya su kimanin 780 da ke karatu a jihar zuwa jihohinsu na asali a wani…

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ta mayar da daliban musaya su kimanin 780 da ke karatu a jihar zuwa jihohinsu na asali a wani mataki na dakile mummunar cutar nan ta COVID-19.

Jami’in Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi Aliyu Yusuf, shi ne ya bayyana hakan a wata takarda da ya raba ga manema labarai.

Takardar ta bayyana cewa Kwamishinan Ilimi Dokta Muhammad Sanusi Kiru, ya bayyana cewa an mayar da daliban wadanda suka fito daga jihohi 17 na Arewacin kasar nan zuwa jihohinsu domin daukar matakan rigakafi ga cutar Coronavirus.
“Kwashe daliban ya biyo bayan matakan da gwamnatin jihar ta dauka na rufe dukkanin makarantun gwamnati da masu zaman kansu da ke fadin jihar don gujewa yaduwar cutar Coronavirus”

Kwamishinan ya kara da cewa, gwamnatin ta yi hakan ne wajen ganin shirin na musayen dalibai da aka sauke su shekaru 30 ana yi ya dore.
A cewar Kwamishinan, ‘An kirkiri shirin na musayar daliban bisa manufar kara inganta alakar hadin kai tsakanin jihohin Arewa da kuma ba wa dalibai damar girmama al’adun wasu mutanen da ke wasu sassa na jihohin Arewa da kuma yin rayuwa a wasu wuraren da ba nasu ba’. In ji shi.