✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Wadanda suka kamu a Najeriya sun haura 7,500

Karin 265 sun kara kamuwa da cutar coronavirus a Najeriya, a cewar hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa NCDC. Alkaluman da NCDC sun nuna kawo…

Karin 265 sun kara kamuwa da cutar coronavirus a Najeriya, a cewar hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa NCDC.

Alkaluman da NCDC sun nuna kawo yanzu mutum 7,526 suka harbu da cutar tun farkon bullarta a Najeriya.

Alkaluman da NCDC ta fitar a daren Asabar sun nun jihar Legas ce ke kan gaba da sabbin masu cutar #COVID19 guda  133.

Sauran jihohin da aka samu karin wadanda suka kamu da cutar su ne: 

  • Oyo – 34
  • Edo – 28
  • Ogun – 23
  • Abuja – 22
  • Filato – 6
  • Kaduna – 5
  • Borno – 3
  • Neja – 3
  • Kwara – 2
  • Bauchi – 2
  • Anambra – 2
  • Inugu – 2

Ya zuwa yanzu mutum 2,174 suka warke daga cutar a kasar, baya ga mutum 221 da cutar ta yi ajalinsu.