✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: ‘Mutum 800 ne za su iya kamuwa a Jigawa’

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na Jigawa ya ce bisa kiyasin masana, mutane 800 ne za su iya kamuwa da cutar COVID-19 a jihar. Ya kara…

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na Jigawa ya ce bisa kiyasin masana, mutane 800 ne za su iya kamuwa da cutar COVID-19 a jihar.

Ya kara da cewa masanan sun yi gargadin cewa idan har hukumomi suka yi sakaci ba su dauki matakan da suka dace na hana yaduwar cutar ba, idan ta fantsama mutane 20,000 ne za su kamu a fadin jihar ta Jigawa.

Gwamnan, wanda ya sanar da hakan ga manema labarai ranar Talata, ya kuma ce mutanen da aka tabbatar sun kamu da coronavirus a jihar sun kai 118, bayan da aka samu karin mutum hudu.

Gwamnan ya kuma sha alwashin bai wa dukkan ma’aikatan lafiyar da ke kula da da masu fama da cutar ta COVID-19 alawus na N15,000 a kullum daga nan har zuwa lokacin da za a dakile annobar.

Ya ci gaba da cewa daga nan zuwa mako biyu masu zuwa gwamnatin jihar za ta samar da cibiyar gwajin cutar, sannan ya yi alkawarin raba wa marasa galihu kayan abinci kyauta a kwaryar Dutse, babban birnin jihar.

Gwaman Badaru ya kuma yi Karin haske game da dokar rufe wuraren wasu harkoki yana mai cewa umarnin gwamnatin na rufe kasuwanni ne kawai bai shafi shagunan sayar da kayan abinci ba.

Ya kuma ce hanin bai shafi manoma da masu ayyuka na musamman ba.

Ya kuma ce malamai za su yin sallar jam’I, amma mamu su ba da tazara a tsakaninsu kamar yadda aka bukata; kuma jami’an lafiya su samar da kayan tsafta a masallatai sannan kowa ya sa takunkumin rufe fuska a masallacin.