✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Rundunar sojin Najeriya ta yi shirin kar-ta-kwana

Hukumomin koli na rundunonin sojin Najeriya sun dauki matakin zama cikin shirin kar-ta-kwana don aiwatar da dokar ta-baci a kasar idan gwamnati ta bayar da…

Hukumomin koli na rundunonin sojin Najeriya sun dauki matakin zama cikin shirin kar-ta-kwana don aiwatar da dokar ta-baci a kasar idan gwamnati ta bayar da umarnin yin haka da nufin hana yaduwar cutar Coronavirus.

Wata majiyar tsaro mai tushe ta shaida wa jaridar Daily Trust cewa an umarci dukkan cibiyoyin soji da ke kasar su zauna cikin shiri don fito da dakaru da zarar an bukaci hakan.

Bayanai dai na nuna cewa ranar Talata aka bayar da wannan umarni ga cibiyoyin na rundunonin soji.

Majiyar ta kuma ce tuni aka umarci manyan kwamandojin Rundunar Sojin Kasa da su fara atisaye don ta da kaimin dakarunsu na gudanar da wannan aikin.

“Za a yi atisayen ne da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro don tabbatar da kowa ya bi”, a cewar majiyar, wadda ba ta so a ambaci sunanta ba.

Ta kuma kara da cewa ana shirye-shiryen samar da manyan motoci na daukar gawarwaki ko da lamarin ka iya kaiwa inna naha.

Ranar Laraba ne dai wasu kafofin yada labarai na intanet suka wallafa wata sanarwar cikin gida da aka ce an samo daga hedkwatar Rundunar Sojin Kasa da ke Abuja, wadda ke nuna cewa rundunar a shirye take ta aiwatar da dokar ta-bacin.

Sai dai kuma rundunar ta fitar da wata sanarwa ta hannun Mukaddashin Daraktan Hulda da Jama’a Kanar Sagir Musa tana musanta labaran da aka bayar cewa za a aiwatar da dokar ta-bacin ranar Juma’a.

“Mummunar fassarar cewa gwamnati za ta ayyana dokar ta-baci ta tsayar da komai a fadin kasar nan sannan ta baza sojoji ranar Juma’a 27 ga watan Maris karya ce mara tushe tsagwaronta”.

Amma Kanar Sagir Musa ya tabbatar da umarni ga Rundunar ta kasasnce cikin shiri ko da cutar za ta kara kazancewa bisa la’akari da abubuwan da ke faruwa a wasu kasashe.

Hakan dai na zuwa ne sa’o’I 72 bayan Ministan Yada Labarai da Al’adu Alhaji Lai Mohammed ya shaida wa manema labarai cewa Kwamitin Cika-Aiki a Kan Cutar Coronavirus ya bayar da shawarar a kara daukar wasu matakai masu tsauri.

“Muna da kyakkyawan fata a yunkurin da muke yi na shawo kan wannan bala’i, amma a shirye muke mu dauki mataki idan al’amura suka kazance”, inji shi.

Ya kuma kara da cewa, “Gaskiyar lamari shi ne abubuwa ka iya kazancewa fiye da yanzu, don haka ana bukatar hada karfi da karfe.

“Akwai yiwuwar daukar matakan da suka fi na yanzu tsauri, amma duk shawarar da aka yanke za ta zama don kare muradun ’yan Najeriya ne”.

A Italiya da wasu kasashen inda cutar ta yi kamari an yi amfani da sojojin wajen aiwatar da dokar ta-bacin da aka ayyana da binne gawarwakin wadanda cutar ta yi ajalinsu da kuma ayyukan jinkai.

Tuni wasu jihohi a Najeriya suka ba da sanarwar hana shigar jama’a yayain da wasu kuma suka kafa dokar hana fita a wasu lokuta.

Zuwa karfe 11.25 na daren ranar Laraba dai a cewar Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya, mutane 51 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar.