✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Sabbin ka’idojin binne gawa a Legas

A wani mataki na dakile yaduwar annobar coronavirus, majalisar masarautar Agege da ke jihar Legas ta fitar da sababbin ka’idojin binne gawa a makabartar Hausawa…

A wani mataki na dakile yaduwar annobar coronavirus, majalisar masarautar Agege da ke jihar Legas ta fitar da sababbin ka’idojin binne gawa a makabartar Hausawa da ke Markaz a yankin.
Magatakardar masarautar ta Agege kuma hakimin yammacin garin, Alhaji Abubakar Ali Na’ibi, ya shaida wa Aminiya cewa masarautar ta takaita yawan masu yi wa gawa rakiya a lokacin jana’iza zuwa mutum 15 kamar yadda gwamnatin Legas ta kayyade, kana ba za a yarda a binne gawa ba har sai an tabbatar da dalilin mutuwar ta.
“Ba za a binne gawa ba sai da takarda daga asibiti domin a san musababbin mutuwar mamacin domin gudun kada a samu yaduwar coronavirus ta hanyar yi wa gawa jana’iza,” inji shi.
Ya kuma ce, “An tanadi matakan kariya a makabartar Agege wadanda suka hada da samar da kayan kariya ga masu hakar kabari, da doka cewa duk wanda zai shiga makabarta sai ya wanke hannayensa da kafafunsa da sinadarin da muka ta nada, haka idan ya fito daga makabartar sai ya maimaita haka”.
Makabartar Agege ce makabarta mafi girma da al’ummar Arewa mazauna Legas ke binne mamatansu a ciki, inda baya ga garin Agege akan kawo mamata daga cikin  garin Legas, da Apapa da sauran sassan Legas da wasu sassan jihar Ogun da ke  makwabtaka.