Da Dumi Dumi

Coronavirus: Shugaban karamar hukumar Jama’a ya gargadi jama’a

Peter Danjuma Averik

Shugaban karamar hukumar Jama’a ta jihar Kaduna, Peter Danjuma Averik, ya gargadi jama’ar yankin da su guji yawan tafiye-tafiye da ba su zama dole ba su kuma nisanci tarurruka don kare kan su daga kamuwa ko yada cutar Coronavirus har zuwa lokacin da za a shawo kan matsalar.

A cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun jami’in yada labarai na karamar hukumar, Simeon Dauda, Mista Averik ya jawo hankalin jama’a cewa duk da babu labarin bullar cutar a yankin da ma jihar Kaduna, lallai ne su kula da tsafta kamar yadda jami’an kiwon lafiya ke bayar da shawara a kai domin an ce rigakafi yafi magani.

Ya yi kira ga jama’a da su gaggauta kai kansu duk wani asibiti mafi kusa a duk lokacin da wani ya ga alamun ciwon da suka hada da: zazzabi da tari da kaikayin makogoro da wahalar numfashi, don samun kulawa ta gaggawa.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya