✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Coronavirus ta kashe mutum 587 a Kano cikin mako biyar’

Gwamnatin Tarayya ta ce binciken kwakwaf din da ta gudanar ya nuna kaso 50 zuwa 60 cikin dari na mutane 979 din da suka mutu…

Gwamnatin Tarayya ta ce binciken kwakwaf din da ta gudanar ya nuna kaso 50 zuwa 60 cikin dari na mutane 979 din da suka mutu a cikin makonni biyar a jihar Kano annobar coronavirus ce ta yi ajalinsu.

Ministan lafiya, Osagie Ehanire ya bayyana hakan yayin jawabin hadin gwiwa na Kwamitin Kar-ta-Kwana da shugaban kasa ya kafa don yaki da cutar karo na 41 ranar Litinin a Abuja.

A cewar ministan, binciken da wani kwamitin kwararru da suka tura jihar ya gudanar ya gano cewa mace-macen sun fi shafar ‘yan sama da shekaru 65, kuma akasarinsu an tabbatar cewa cutar ce ta yi ajalinsu.

 

Me hakan ke nufi?

Ya ce hakan na nufin akalla mutum 587 ne suka mutu a Kanon, adadin da ya zarce mutum 354 din da suka mutu a jihohi 35 da Babban Birnin Tarayya Abuja zuwa ranar Litinin, kamar yadda alkaluman Hukumar Kula da Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC suka tabbatar.

Zuwa yanzu dai NCDC ba ta kai ga shigar da wadannan alkaluman cikin adadin mutanen da cutar ta hallaka ba, wanda ke nuna cewa zuwa ranar Litinin mutum 48 ne suka rasu a jihar Kano sakamakon cutar.

Ministan ya kuma jinjina wa kwamitin kwararrun da suka gudanar da binciken karkashin jagorancin Dakta Sani Gwarzo da Farfesa Abdussalam Nasidi bisa namijin kokarinsu. 

Idan dai za a iya tunawa a ‘yan makonnin da suka gabata, an yi ta zaman dar-dar sakamakon yawan mace-macen da aka yi ta samu musamman ma na fitattun mutane a jihohin Kano da Jigawa da ma wasu jihohin.

Yadda binciken ya gudana
Da yake bayani kan hanyoyin da suka bi wajen tantance wadannan alkaluman, ministan ya ce, “Game da batun yawan mace-macen da aka samu a Kano a tsawon makonni biyar, kawamitin ya tabbatar da mutane 979 ne suka mutu a cikin kananan hukumomin kwaryar birnin Kano.

“Akalla mutum 43 ne suka rika rasuwa a kullum, bayan kirga yawan kaburburan da aka binne su.

“Lamarin ya fi tsanani ne a mako na biyu a watan Aprilu, zuwa karshen watan. Daga nan kuma sai alkaluman suka fara sauka har suka dawo zuwa mutum 11 ne ke mutuwa a kullum.

“Wannan kuma shi ne dama tsaka-tsakin mutanen da suka saba mutuwa a jihar a kullum”, in ji ministan.

‘Akasarinsu a gida suka mutu’
Ya kuma ce binciken kwakwaf din da suka gudanar ta hanyar zantawa da iyalan mamatan ya nuna cewa kaso 56 na mace-macen sun auku ne a gida, yayin da kaso 38 kuma a asibiti suka rasu.

Ministan ya kuma yaba wa gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje bisa ga hadin kai da goyon bayan da ya ba kwamitin a tsawon lokacin da suka dauka suna gudanar da binciken kuma har su ka kammala ba a sami ko mutum daya a cikinsu ya kamu da cutar ba.

A lokacin da mace-macen suka yi kamari dai rahotanni sun nuna yadda ma’aikatan lafiya a jihar suka rika cika wandonsu da iska daga asibitoci bayan wasu abokan aikinsu na ta kamuwa da cutar a yayin da suke kokarin ceto rayukan jama’a.

 Hakan ya tilasta wa mutane da dama masu fama da wasu cututtukan masu bukatar tallafi a kai a kai kamar hawan jinni, cutar suga, ciwon zuciya, da cutar koda da ma wasu cututtukan suka fuskanci kalubale matuka wajen samun cikakkiyar kulawa kamar yadda suka saba samu.