✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Wadanda suka kamu sun kai 139

An samu karin mutum hudu da aka tabbatar sun kamu da cutar Coronavirus a Najeriya, lamarin da ya sa adadin ya kai 139. A cewar…

An samu karin mutum hudu da aka tabbatar sun kamu da cutar Coronavirus a Najeriya, lamarin da ya sa adadin ya kai 139.

A cewar Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) uku daga cikin sabbin kamuwar a Yankin Babban Birnin Tarayya suke, guda kuma a Legas.

“Zuwa karfe 8.00 na daren 31 ga watan Maris, an tabbatar da mutane 139 sun kamu, yayin da aka sallami mutum tara daga ciki biyu kuma suka riga mu gidan gaskiya”, inji sanarwar da hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter.

Wannan alkaluma sun kawo jimillar mutanen da aka tabbatar sun kamu a ranar 31 ga wata zuwa takwas.

Ranar Litinin 30 ga wata ce dai aka samu karuwa mafi yawa a yini guda, inda aka sanar da samun sabbin masu dauke da cutar har mutum 20.

Jihar Legas ce ke da kashi 60 cikin dari na wadanda aka tabbatar sun kamu, yayin da Yankin Babban Birnin Tarayya ke da kashi 19 cikin dari.