✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Yawan wadanda suka kamu ya kai 135

Adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da Coronavirus a Najeriya ya karu zuwa 135. Adadin ya karu ne bayan da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu…

Adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da Coronavirus a Najeriya ya karu zuwa 135.

Adadin ya karu ne bayan da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta sanar da samun karin mutum hudu ranar Talata.

“An bayar da rahoton samun sabbin kamuwa da COVID-19 a Najeriya mutum hudu, mutum uku a Jihar Osun, daya a Jihar Ogun.

“Zuwa karfe 11.15 na ranar 31 ga watan Maris, an tabbatar da mutane 135 sun kamu, yayin da mutum biyu daga ciki suka riga mu gidan gaskiy”, inji sanarwar da hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter.

Wannan sanarwa na zuwa ne a rana ta farko da fara aiki da dokar hana fita a Legas da Abuja, wuraren da suka fi yawan wadanda aka tabbatar sun kamu.

Ranar Litinin 30 ga wata ce dai aka samu karuwa mafi yawa a yini guda, inda aka sanar da samun sabbin masu dauke da cutar har mutum 20.

Jihar Legas ce ke da kashi 60 cikin dari na wadanda aka tabbatar sun kamu, yayin da Yankin Babban Birnin Tarayya ke da kashi 19 cikin dari.