✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Za a fitar da almajirai 4,443 daga jihar Nasarawa

Gwamnatin jihar Nasarawa ta kammala shirye-shiryen mayar da almajirai 4,443 zuwa jihohinsu na asali. Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa za a kwashe almajiran,…

Gwamnatin jihar Nasarawa ta kammala shirye-shiryen mayar da almajirai 4,443 zuwa jihohinsu na asali.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa za a kwashe almajiran, wadanda ba ‘yan asalin jihar ba ne, a mika su ga danginsu.

Majiyar ta kara da cewa gwamnatin ta gama shirya motocin da za su yi jigilar almajiran a ‘yan kwanaki masu zuwa.

Gwamnatin za ta mayar da almajiran zuwa jihohi 19 da Yankin Babban Birnin Tarayya Abuja.

Almajirai 207 za a mayar  jihar Adamawa, 701 Bauchi,  34  Binuwai, 24 Borno, 55  Gombe , 273  Jigawa, da kuma guda daya da za a kai jihar Enugu.

Sauran sun hada da 417 da za a kai  Kaduna,  1,497 Kano,  689 Katsina,  208 Kebbi, 35 Kogi, 13 Kwara , 76 Niger, 3 Oyo, 160 Filato, 48 Sakkwato,  102 Taraba, 49 Yobe, 219 Zamfara  da kuma daya da za a mayar Yankin Babban Birnin Tarayya.

A gefe guda kuma, almajirai 24,005 za a mayar  wurin iyayensu a fadin jihar ta Nasarawa.

Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Ahmad Tijjani Aliyu, ya ce a wani taro da suka gudanar ta yanar gizo, gwamnonin jihohin arewacin Najeriya sun amince da mayar da almajirai zuwa jihohinsu na asali saboda su samu kulawar iyayensu.