✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Za a rufe iyakokin Kano ranar Juma’a

A kokarinta na dakile yaduwar cutar coronavirus, Gwamnatin Jihar Kano za ta rufe dukkanin hanyoyin shigowa jihar daga karfe 12 na daren ranar Juma’a. Daga…

A kokarinta na dakile yaduwar cutar coronavirus, Gwamnatin Jihar Kano za ta rufe dukkanin hanyoyin shigowa jihar daga karfe 12 na daren ranar Juma’a.

Daga wannan lokaci za a dakatar da shige da fice a jihar wanda ya shafi har masu shigowa jihar ta filin jirgin saman Malam Aminu Kano, idan mutane suka sauka sai dai su zauna a filin jirgin domin ba za su sami hanyar shigowa cikin jihar ba.

Gwamnan Jihar Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ya jaddada cewa “Daukar matakin ya zama dole domin zai taimaka wajen kokarin da jihar ke yi na ganin cutar ta coronavirus ba ta bazu a jihar ba.”

Gwamnan ya yi kira ga jama’a da su yi hakuri da halin da aka sami kai a ciki na damuwa.

A cewar Gwamnan, gwamnatin tana daukar duk matakan da suka kamata wajen ganin cutar ba ta sami wurin zama a jihar ba.

Gwamnan ya yi kira ga jama’ar jihar da su zama masu bin doka musamman ma’aikata da aka umarce su su zauna a gida tare da yin aiki da shawarwarin likitoci.

Gwamnan ya ce, gwamnatin za ta sanar da al’ummar jihar halin da ake ciki ko da za a sami bullar wata alamar cutar a jihar, lamarin da ba a fata.