✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Zaman zulumi a Bauchi, gwamna ya killace kansa

An shiga zaman zullumi a Bauchi bayan da gwamnan jihar, Bala Mohammed, da kwamishinoninsa guda biyu suka killace kansu sakamakon mu’amala da dan tsohon Mataimakin…

An shiga zaman zullumi a Bauchi bayan da gwamnan jihar, Bala Mohammed, da kwamishinoninsa guda biyu suka killace kansu sakamakon mu’amala da dan tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, wanda aka tabbatar yana dauke da cutar Coronavirus.

Wata sanarwa mai dauke da sa-hannun babban mai bai wa gwamnan shawara a kan kafofin yada labarai Mukhtar Gidado ta tabbatar da hakan.

“Wannan mataki [da gwamnan ya dauka] ya biyo bayan wata sanarwa ne daga Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) cewa gwaji ya tabbatar dan tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Mohammed Atiku Abubakar, yana dauke da cutar Coronavirus bayan dawowarsa daga wata tafiya zuwa kasashen waje”, a cewar Gidado.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnan ya shigo jirgi daya da Mohammed Atiku Abubakar daga Legas kuma har sun yi hannu suna ta raha.

“Zuwa yanzu dai gwamnan bai nuna wasu alamun kamuwa ba, amma bisa shawarar NCDC zai killace kansa don kauce wa yiwuwar yada cutar”, inji sanarwar.

Sai dai tuni hankulan wasu mutane, musamman jami’an gwamnati da suka yi mu’amala da shi a karshen makon jiya, suka tashi.

Da safiyar ranar Litinin ne dai tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya sanar da kwantar da Mohammed a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja.

Hukumar NCDC ta ce zuwa karfe 10 na safiyar Litinin mutum 36 aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya.

Mutum guda daga cikinsu kuma ya riga mu gidan gaskiya, yayin da aka salami mutum biyu bayan sun warke.