Da Dumi Dumi

An tsawaita dokar hana sufurin jiragen sama a Najeriya

Filin jirgin saman Murtala-Muhammed-International-Airport-MMIA-Lagos

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta tsawaita dokar hana sauka da tsahin jiragen sama a fadin kasar da karin mako hudu, a kokarin ta na dakile yaduwar cutar COVID-19.

Sakataren Gwamnatin Tarayyar Najeriya Boss Mustapha, ne ya sanar da haka a sa’ilin da yake gabatar da jawabin da yakan yi a kowace rana dangane da annobar.

Boss Mustapha, wanda shi ne shugaban kwamintin kar ta kwana mai yaki da cutar na  gwamnatin tarayya, ya shaida cewa gwamnatin ta dauki matakin ne biyo bayan shawarwarin da masana a fannin suka bata.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya