✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: A yi biyayya ga gwamnati —Masana

Wasu masana harkar lafiyar al’umma sun yi gargadin cewa muddin ’yan Najeriya ba su yi biyayya ga umarnin da gwamnatoci a matakan tarayya da jihohi…

Wasu masana harkar lafiyar al’umma sun yi gargadin cewa muddin ’yan Najeriya ba su yi biyayya ga umarnin da gwamnatoci a matakan tarayya da jihohi ke bayarwa na zaman gida don hana cutar coronavirus yaduwa ba, to duk fafutukar da aka yi zuwa yanzu za ta tashi a banza.

Daya daga cikin masanan, Tunji Olarinde, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) hannu daya ba ya daukar jinka don haka wajibi ne a hada karfi da karfe gaba daya a yaki cutar.

“Wannan alhaki ne da ya rataya a wuyan kowa, kuma wajibi ne ’yan Najeriya su yi abin da ya dace su karbi wannan sabon tsarin rayuwa domin mu gudu tare mu tsira tare”, inji Mista Olarinde.

Masanin ya kuma ce bay aga bin umarnin gwamnatoci da hukumomin lafiya, akwai wata rawar da ‘’yan Najeriya za su taka.

“Wajibi ne mu rika wanke hannuwanmu a kai a kai da sabulu da ruwa mai gudana sannan mu rika yin nesa da juna.

“Haka kuma dole ne mu taimaka wajen yada sahihan bayanai don fadakar da sauran mutane. Wajibi ne mu yi watsi da labaran kanzon kurege saboda zai iya haddasa rudani”, inji shi.

Olarinde ya koka da yadda ake yi wa dokokin hana fitar karan-tsaye, yana cewa “rayuwa ta fi komai muhimmanci”.

“Mu daure mu yi biyayya ga gwamnati yanzu saboda mu rayu kuma rayuwarmu ta yi kyau gobe.

“Idan muka yi biyayya hakar gwamnati da hukumomin lafiya za ta cimma ruwa kuma annobar ta zo karshe nan ba da jimawa ba”

Ranar Litinin ne dai Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da sanarwar tsawaita dokar hana fita da aka ayyana a jihohin Legas da Ogun, da ma Yankin Babban Birnin Tarayya.

Jihohin Najeriya da dama ma sun kafa dokar takaita zirga-zirga ko ma hana fita gaba daya.

Sai dai ’yan Najeriya da dama na kukan cewa zaman gida ba zai yiwu ba tun da sai sun fita za su samu abin da za su ci, ga shi taimakon da gwamnati ta yi alakawarin bayarwa ba ya kaiwa gare su, ko kuma bai taka kara ya karya ba.