✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: An sanya dokar hana fita a Kano

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da sanarwar sanya dokar hana fita a fadin jihar na tsawon mako guda. Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana…

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da sanarwar sanya dokar hana fita a fadin jihar na tsawon mako guda.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana haka a lokacin da ya yi wa jama’ar jihar jawabi.

Gwamnan ya ce dokar za ta fara aiki ne da karfe 10 na daren Alhamis.

Ranar Talata ne dai Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta bayar da sanarwar samun karin mutum daya wanda ke dauke da cutar COVID-19.

Kwamishinan Lafiya Dokta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya tabbatar da hakan.

Samun karin mutum daya da aka yi  ya sa adadin mutanen da suka kamu a jihar ya kai hudu.

Ranar Asabar aka tabbatar da samu mutum na farko, wani jami’in diflomasiyya da ya yi ritaya, wanda aka ce ya yi tafiye-tafiye zuwa Legas, da Abuja, da Kaduna.