✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Arik ya rage albashin ma’aikata da kashi 80

Kamfanin jiragen sama na Arik, wanda daya ne daga cikin manyan kamfanonin jiragen sama a Najeriya, ya sanar da rage albashin ma’aikata da kashi 80…

Kamfanin jiragen sama na Arik, wanda daya ne daga cikin manyan kamfanonin jiragen sama a Najeriya, ya sanar da rage albashin ma’aikata da kashi 80 cikin 100 daga wannan watan Afrilu.

Sannan kuma daga ranar 1 ga watan Mayu ma’aikata kashi 90 cikin 100 za su tafi hutu ba albashi, har sai abin da hali ya yi.

Wani sako da Babban Daraktan kamfanin Roy Ilegbodutura wa ma’aikatan ya bayyana cewa an rage albashin ne saboda kudin shigar da kamfanin ke samu ya ragu da kashi 98 cikin 100, da kuma faduwar darajar Naira.

Tun bayan da annobar COVID-19 ta barke ne dai kamfanonin jiragen sama a Najeriya suka shiga tsaka mai wuya, lamarin da ya tilasta musu dakatar da ayyukansu kusan wata guda da ya gabata.

Kungiyar masu kamfanonin jiragen sama ta Najeriya (AON), wadda kamfanonin jiragen sama na gida ke karkashin tutarta, ta bukaci agajin gaggawa daga gwamnati.

A cewar kungiyar ta AON kamfanonin na gida sun yi asarar Naira biliyan 360 tun lokacin da suka fara dakatar da ayyukan na su.

Ma’aikatan kamfanin na Arik sun nuna kaduwa da jin wannan sanrwa, ganin cewa yanzu kamfanin yana karkashin kulawar hukumar saye basussukan da suka yi tauri AMCON ne.

A watan Fabrairun 2017 ne hukumar ta AMCON ta karbi ragamar gudanar da kamfanin daga hannun wadanda suka mallake shi tun asali.